in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sako daga malam Abba Muhammad Nuhu a Kano, Nijeriya kan faretin sojan kasar Sin
2015-09-07 18:41:43 cri
Assalam Alaikum,

Bayan miliyoyin gaisuwa mai yawa.Yaya aiki?Ya hakuri da mu?Mun gode kwarai.

Bayan haka na yi matukar farin ciki dan ganin faretin da sojojin kasar Sin da suka yi,a ranar 3 ga Satumba.A gaskiya sun burge.Wannan ya nuna wa sauran kasashe cewar kasar Sin ta kawo karfi. Yanzu itama ta kamata a sata acikin kasashen da ake kira da [super powers].Ina ma shugaba Mao yana da rai da yaga yadda Sinawa suka jajir ce,suka jure wa wahalhalu da kuma hakuri akan abubuwan da suka same su acan baya.Allah ya karawa kasar Sin da jama'arta lafiya,karuwar arziki,wadata,kwanciyar hankali da koshin lafiya.Kuma Allah ya ja zamnin kasar Sin.Allah ya ja zamnin jama'ar kasar Sin.

Ni a ra'ayina game da wannan faretin da sojojin kasar Sin ta nuna wa Duniya,shi ne Kasar Sin ta kara kera wadansu makaman domin ta kare kanta daga duk wani hari da wata kasa take da niyyar kawo mata.Kuma na ji shugaba Xi ya ce zai rage yawan sojojin kasar Sin 300.000.Don Allah a gaya masa ka da ya yi hakan.Domin kasashen yamma suna tsoron Sin saboda yawan jama'arta.

A karshe ina taya Sinawa murnar cika shekaru 70 da cin nasarar fatattakan azzaluman Jafanawa.Allah ya kara wa kasar Sin kwarin gwiwa da tattalin arziki. A karshe ina gai da dukkan ma'aikatan CRI.Don Allah ku aikomin da mujalla mai dauke da wannan faretin da aka gabatar

A huta lafiya,

Abba Muhammad Nuhu

Kano Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China