in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Lardin Gansu mai ban sha'awa
2015-08-09 17:43:45 cri
Zuwa ga sashen Hausa nan CRI.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa na Rediyon kasar Sin suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda na ke lafiya a nan birnin Kano. Bayana haka, na samu damar sauraron kashi na farko da kashi na biyu na shirin 'Allah daya gari bamban' a ranekun 31 ga watan Yuli da kuma 7 ga watan Agusta, 2015. Inda Malamai Lubababtu Lei da Maman Ada suka zanta da Maryam Yang, daya daga cikin ma'aikatan sashen Hausa da ta samu ziyaratar lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin.

Ba shakka, wannan shiri ya burge ni sosai musamman yadda na samu karin ilimi dangane da lardin Gansu wanda bai yi fice sosai ba kamar sauran biranen kasar Sin kamar Beijing, Shanghai, Xi'an, da sauransu. Amma yanzu na fahimci cewa, lardin Gansu na da dimbin tarihi da kuma ni'imar da ta dace da yawon shakatawa, bayan da na saurari wannan tattaunawa da malama Maryam Yang. Hakika, yanzu na fahimci cewa, lardin na Gansu na daya daga cikin lardunan kasar Sin da suka kunshi al'ummar Musulmi, musamman yadda aka bayyana cewa, a birnin Lanzhou hedkwatar lardin na Gansu a na sarrafa kayayyakin halittu na halal a wata shiyyar masana'antu domin biyan bukatun al'ummar Musulmi. Wannan batu na kayayyakin halittu na halal a lardin wata kyakkyawar amsa ce ga masu zargin cewa, Musulmi ba sa iya ibadar Azumi a kasar Sin. Domin rahoton ya tabbatar da cewa, al'ummar Musulmi na zaman 'yanci da walwala, kuma suna samun duk wasu kayayyakin halal da suke bukata na yau da kullum ba tare da shan wata wahala ba. Abin burgewa da kayayyakin halittu na halal na birnin Lanzhou shi ne, yadda a ke iya fitar da kayan zuwa kasashen dake kudancin Asiya, wanda hakan ke nuna suna iya sarrafa kayayyakin halittu na halal fiye da bukatunsu.

Hakika, yanzu na fahimci cewa a lardin na Gansu ba wai kawai birnin Lanzhou ne ya samu bunkasuwa ba, har ma da birnin Zhangye, wanda mu ka saurari bayanai dangane da irin ci gaban da birnin ya samu ta fannin noman zamani dake samar wa birnin isashen kayan abinci da sauran kayayyakin lambu. Wani abu da ya kara burge ni da birnin Zhangye shi ne, arzikin dabbobi da suka hadar da shanu da kuma tumaki da awaki, wato kananan dabbobi. A ra'ayi na, birnin Zhangye yana yin kamanceceniya da yanayin Xinjiang wanda ke da dimbin al'ummar Musulmi makiyaya.

Wani abu da na kara fahimta kuma ya burge ni da lardin na Gansu shi ne, batun samar da kayayyakin more rayuwa, musamman yadda gwamnatin kasar Sin ta samar da jirgin kasa mai sauri daga birnin Lanzhou fadar gwamnatin lardin na Gansu zuwa birnin Zhangye, wanda ya rage tsahon lokacin tafiya tsakanin biranen biyu daga sa'oi 10 zuwa sa'oi uke kawai. Hakika, ko tantama babu, wannan jirgi mai sauri zai taimaka matuka wajen saukaka zirga-zirga da kuma kawo tasiri ta fuskar bunkasar tattalin arziki.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China