Tare da fatan dukkan ma'aikatan ku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, na aiko da wannan sako domin na gabatar da sakon jaje na dangane da bala'in fashe fashen abubuwa da ya haddasa gagarumar gobara a birnin Tianjin da ke gabashin kasar Sin.
Hakika, ina taya al'ummar Sinawa jimami da bakin cikin aukuwar wannan lamari ba zato ba tsammani wanda tuni ya lakume rayukan fiye da mutane 100 da kuma jikkata fiye da 700. Ina fatan iyalan wadanda wannan hatsari ya rutsa da su za su hakuri da juriyar rashi na dukiya da kuma rayukan da aka yi. Da fatan masu aikin ceto za su kara kokarin da suke yi don ganin wannan kasaitaccen birnin na Tianjin mai matukar tasiri ta fuskar tattalin arziki ya dawo hayyacin sa cikin sauri. Na gode.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria