Jin cewa, lardin Gansu dake arewa masu yammacin kasar Sin yana da yawan musulmai akalla milyan daya da dubu dari takwas(1,800,000,000) wani abun alfahari ne ga al'ummar musulmai na kasar Sin da ma sauran al'ummar musulmai da muke fadin duniya. Banda wannan, lardin Gansu ya yi kaurin suna a dud duniya wajen kyan yanayi da ratsin ciyaye kore shar masu ban sha'awa kana kuma ga muhimman guraren tarishi dake da dogon tarishi sosai. Hakika lardin Gansu na burgeni kuma yana ban sha'awa sosai kuma ina da yakinin cewa, lardin Gansu na matukar jan hankalin milyoyin mutane dake nuna kuzari da himma wajen yin rigegeniya zuwa kasar Sin dan yawan shakatawa da yawan bude idanu da ziyartar muhimman guraren tarishi dadaddu da suka shahara a fagen tarishi a kasar Sin. Banda lardin Gansu dake da yawan musulmi a kasar Sin, akwai jihohin Ningzia da Xi'an da kuma Xinjiang inda musulmi ke da matukar rinjaye kana ga muhimman guraren cin abuncin halal na musulmai kana kuma akwai kyan yanayi sosai da kuma muhimman guraren yawan shakatawa da bude idanu har wa yau, jihohin 3 suna da muhimman guraren tarishi da suka dade sosai. Ni dai, a matsayina na musulmai ina da sha'awar kai ziyara ko yawan shakatawa a wayannan muhimman gurare dan kashe kwarkwatar idanu da kuma sada zumunci da yan uwanmu musulmai a lardin Gansu da jihohin Ningzia da Xi'an da Xinjiang da sauran guraren tarishi da suka shahara a kasar Sin irinsu: Ganuwar kasar Sin(great wall) lardin Sichuan da yankunan masamman na Macao, Taiwan da Hongkong da tsibirin Diaoyu na kasar Sin da kuma Dandalin tunawa da madugun gina sabuwar kasar Sin Marigayi Mao Zadang da dai sauransu. Ina fata kasar Sin da al'ummarta sinawa za su ci gaba da samun bunkasuwa cikin hanzari yadda yakamata sosai kana ina fatan samun bunkasuwar hadin gwiwa tskanin nahiyar Sin da kasashenmu na Afirka masu tasowa, amin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua