in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sako daga malam Nuraddeen Ibrahim Adam kan faretin soja na kasar Sin
2015-09-02 08:40:00 cri
Tare da fatan baki dayan ma'aikatan ku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda na ke lafiya.

Bayan haka, yayin da a ke daf da gudanar da gagrumin bikin faretin sojoji a dandalinTian'anmen a gobe Alhamis 3 ga watan Satumba, kasar Sin ta riga ta dauki hankalin duniya, sakamakon yadda tun a makon da ya gabata kafafen yada labarai musamman tashar talbijin ta kasar Sin wato CCTV News ke kawo rahotanni dangane da yadda a ke shirye shiryen bikin da kuma gwajin faretin sojoji. Hakika, kasar Sin ta yi fice wajen gudanar da irin wannan biki, sai dai bikin na bana da alama ya sha bamban da na baya, saboda yadda shugabannin kasashen duniya fiye da 10 za su samu halattarsa. Ban da wannan kuma, bikin zai kasance ma fi kasaita a tarihi, saboda kasar Sin za ta baje kolin wasu makaman yaki da sauran kayan fusaha na zamani a karon farko, don fahimtar da al'umma irin ci gaban fusaha da kasar Sin ke da shi.

Wani abu da ya kara jan hankali na dangane da wannan biki shi ne, ya na dakarun soji na wasu kasashen daban za su shiga jerin gwanon sojijin kasar Sin yayin bikin faretin da zai ratsa makeken titin Chang'an da kuma dandalin Tian'anmen. Ba shakka, ba saba ganin sojojin wata kasa a biki irin wannan ba a tarihin kafuwar sabuwar kasar Sin. Amma abin lura a nan shi ne, sojojin kasashen waje da suka halarci wannan biki suna nuna goyon bayansu ne ga kasar Sin da kuma taya kasar ta Sin murnar cika shekaru 70 na nuna tirjiya ga harin Japanawa tare da yaki da masu halayyar nuna karfin tuwo a duniya.

Hakika, gudanar da irin wannan biki ya dace, domin zai sa a rika tunawa da 'yan mazan jiya wadanda suka kwanta dama bayan sun sadaukar da rayukansu wajen kare kasa. Sa'an nan, akwai darussa masu yawa da za a koya idan a na waiwayen abubuwan da suka wakana yayin yakin duniya na biyu, wanda ya hada da martaba juna, fifita zaman lafiya fiye da komai, da kuma warware duk wata matsala ko tankiya ta hanyar yin shawarwari a kan tebur maimakon zubar da jini.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China