Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ga baki dayan ma'aikatan ku a birnin Beijing, ina fatan duk kuna cikin koshin lafiya. Bayan haka, yau Laraba 5 ga watan Agusta, na samu ikon sauraron maimaicin shirin ku na 'Gani Ya Kori Ji' wanda Malamai Maman Ada da Saminu Alhassan bisa jagorancin Ibrahim Yaya suka gabatar da tattaunawa tare da bayyana mabambantan ra'ayoyi dangane da ziyarar shugaba Barrack Obama a nahiyar Afirka.
Koda yake, malaman sun tattauna alfanu da ma akasin haka dangane da ziyarar shugaban a Afirka, amma duk da haka, ra'ayi na ya dan sha bamban da na malaman. Domin ni a ganina akwai wata boyayyiyar manufa da kasar Amurka ke son cimma a nahiyar musamman yada angizon manufofi na 'yan jari hujja ba wai taimaka wa kasashen nahiyar ta Afirka ba da ke cikin yanayin hannu baka hannu kwarya ba. Watakila ma ziyarar na da alaka da yadda kasar ta amurka ke nuna kishi ga kasar Sin bisa la'akari da yadda kasar Sin ke ci gaba da samun karbuwa a nahiyar ta Afirka.
Ita dai kasar Amurka, ungulu ce da ba ta yin jewar banza, duk inda ka ga tana lekawa to ko shakka babu akwai abin da ta hango. Domin ko a baya bayan nan, sai bayan da shugaban Nijeriya ya isa Amurka bisa gayyata ta musamman sannan manufar gayyatar ta fito fili lokacin da kiri-kiri shugaba Obama ya gabatar da bukatar Amurka ga shugaba Buhari kan auren jinsi, wanda ko kusa ba shi ne a gaban Nijeriya ba, illa batun farfado da tattalin arziki da kuma yaki da 'yan ta da kayar baya da suka addabi kasar ta Nijeriya. Wato Amurka na nufin, har sai Nijeriya ta amince da auren jinsi kafin su ba ta taimako ta fanni tsaro.
Abin ban mamaki da ban takaici, har yanzu ban ji ita kasar ta Amurka ta tallata wannan haja ta ta ga abokiyar burminta ba, wato kasar Isra'ila, wacce take a matsayin sha-lele, ita kadai da za raba gatancinta a wajen Amurka ga kasashen Afirka baki dayansu, to da kakarsu ta yanke saka.
Na gode.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria