Bayan haka, ina mai cike da farin cikin gabatar da wannan wasika domin sanar da ku cewa na samu kyautar Radio ta musamman da ku ka aiko min ranarTalata 28 ga watan Yuli, 2015. Hakika, na yi farin ciki sosai da samun wannan kyauta a matsayina na mai sauraron Radio yau da kullum. Ko shakka babu, kyautar Radio kyauta ce mai matukar muhimmanci da daraja ga mai sauraro, kasancewa duk mai sauraro na gaske ba ya taba rabuwa da Radio a kowacce rana saboda yadda Radio kan samar da bayanai masu muhimmanci ga rayuwar dan Adam, kamar labarai, rahotanni, batun siyasa da tattalin arziki, sanao'in hannu, kiwon lafiya da dai sauransu.
Hakika, ba zan taba mantawa da gudunmawar sashen Hausa na CRI ta wannan fanni ba, domin wannan shi ne karo na 4 da sashen Hausa suka bani kyuatar akwatun Radio cikin shekaru 25, wato na samu kyautar Radio ta farko ne a shekarar 1990 lokacin da Radio Beijing suka shirya gasar samun kyautoci kan bikin wasannin kasashen Asiya na 11 da aka gudanar a birnin na Beijing.
Na gode muku kwarai da gaske kuma da fatan zumunci zai ci gaba da habaka tsakanin mu.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria