Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ga ma'aikatan ku, ina fatan duk kuna lafiya. Bayan haka, ina taya birnin Beijing murnar samun izinin shirya gasar wasannin Olympic na yanayin hunturu a shekarar 2022. Hakika, tun kafin a kai ga kada kuri'ar zaben birnin da zai karbi bakuncin wasannin masu sharhi da nazarin al'amuran yau da kullum ke hasashen cewa, birnin Beijing ne zai samu nasara. Haka kuwa lamarin ya kasance, wannan kuwa bai kamata ya zama wani abin mamaki ba. Saboda wasannin Olympic na yanayin zafi da birnin Beijing ya samu shiryawa a shekarar 2008 ya ja hankalin duniya sosai, har wasu na ganin cewa, ba a taba shirya kasaitaccen bikin bude wasannin na Olympic a duniya ba kamar irin na birnin Beijing.
Ban da wannan, kowa shaida ne cewa, birnin Almaty ko kusa bai kai birnin Beijing ci gaba ba, sa'an nan birnin Beijing na samun ci gaba cikin sauri ta yadda birnin ya tanadi duk wasu kayayyakin more rayuwa irin na zamani. Kazalika, akwai kyakkyawan fatan cewa, matsayin birnin Beijing zai karu wajen ci gaban zamani kafin shekarar 2022 ta yadda duk wasu abubuwan da ake bukata dangane da wasan na Olympic. Ina fatan birnin Beijing zai bai wa mara da kunya ta yadda zai shirya wasannin hunturu mai armashin da zai ja hankalin duniya kamar yadda ya yi a shekarar 2008 yayin wasannin Olympic na yanayin zafi.
Na gode.
Mai sauraronku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria