Cikin farin ciki ina taya al'ummar kasar Sin masamman ma mutanen birnin Beijing da gwamnatin kasar Sin bisa nasarar da birnin Beijing ya samu na shirya wasannin olympic na duniya a yanayin sanyi. Agaskiya ayarin masu aikin tantance birnin da zai shirya wasannin winter olympic games na 2022, sun yi dogon tunani da hangen nesa da suka zabi birnin Beijing na kasar Sin a matsayin birnin da ya samu zarafin shirya wasannin olympic na duniya a 2022. A birnin Beijing ya cancanci matsayin da ya kara samu na zarafin shirya wasannin olympic na duniya a 2022, ko a shekarar 2008 ma sai da birnin Beijing na kasar Sin ya samu zarafin shirya gasar wasannin Olympic na duniya a yanayin zafi wanda kuma birnin Beijing din yayi nasarar shiryawa da kammalawa inda kuma dud duniya suka yaba da sahihancin birnin Beijing din na samun damar shirya gasar olympic na duniya a yanayin zafi a 2008. Birnin Beijing a 2022.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.