in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakon jaje kan hadarin jirgin ruwa a Sin
2015-06-03 14:52:32 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri ga ma'aikatan ku baki daya, ina fatan duk kuna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, cike da alhini da tausayi na ke gabatar da wannan sako don jajantawa al'ummar Sinawa baki daya bisa aukuwar wani mummunar hadarin jirgin ruwa da wata mahaukaciyar guguwar teku ta haddasa a kogin Yangtze ranar Litinin 1 ga watan Yuni, lamarin da ya kawo asarar kimanin rayuka 400 ko fiye.

Da fatan wadanda suka rasa 'yan uwa ko dangi cikin wannan hadari za su samu karfin zuciyar jurewa, tare da fatan ba za a sake samun aukuwar irin wannan bala'i ba nan gaba. Ina kuma fatan ma'aikatan linkaya da nutsu a cikin teku za su kara kwazon aikin ceto ka za a kara ceto wasu fasinjoji da rai.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
ga wasu
v Ranar yara ta duniya 2015-06-02 16:22:16
v An kammala mika mulki ga sabuwar gwamnatin Gen. Muhammadu Buhari, cikin nasara 2015-05-31 15:54:12
v Sanarwa! 2015-05-26 09:20:48
v Sabon jaddawalin shiraruwan cri hausa na shekara ta 2015 2015-05-26 09:18:22
v Gaisuwa 2015-05-21 20:20:13
v Sabon lokaci! 2015-05-19 15:41:39
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China