Ranar juma'a 29 ga watan Mayu shekara ta 2015, ta kasance wata muhimmiyar rana mai cike da tarishi a taraiyar Nigeria, inda aka yi nasarar mika mulkin kasa ga zababben shugaban kasa Gen. Muhammadu Buhari tare da mataimakinsa Prof. Yemi Osibanjo. Wannan babban abun yaba ne a tarishin kasashenmu na Afirka inda galibi idan mutum ya fadi a zabe, baya amuncewa ya sha kasa. Kamar yadda na saurari jawabinsa, shugaban kasa Gen. Muhammadu Buhari, ya ce zai maida hankali sosai ga batun yaki da cin hanci da rashawa. To, idan mu ka yi dubi sosai bisa wannan saban shiri na saban shugaban kasa Gen. Muhammadu Buhari, muna fata gwamnatin kasar Sin za su yi hadin gwiwa ta fannin yaki da cin hanci a taraiyar Nigeria ganin yadda sabbin shugabannin kasar Sin suka nace bisa dagewa ga kawar da cin hanci da rashawa a kasar Sin kuma kasar Sin tana maida hankali tare da sa muhimmanci ga aiwatar da hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da laifin cin amanar kasa(cin hanci) duk kudinsa kuma duk mukamunsa a kasar Sin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.