Masu iya magana na cewa, 'yawan gaisuwa, yafi yawan fada'. Saboda haka, ina fata ba zaku gaji da ni ba domin kuwa ga sakon gaisuwa ta musamman zuwa gare ku.
Cikin shekaru da dama da na fara sauraren shirye-shiryenku, da ni da sauran masu sauraronku mun samu karuwar ilimi da fahimta a fannoni masu yawan gaske musamman a bayanai da suka danganci kasar Sin da Nahiyar Asiya baki daya.
Ni dai babu abinda zan ce muku, sai fatan alheri bisa kokari da himma da kukan bayar wajen zakulo muhimman bayanai da kuma yada su domin fahimtar da al'ummar kasa ta Najeria, da ma na wasu kasashen duniya baki daya.
A karshe, ina fata malama Fatima zata isar da gaisuwata zuwa ga duk kan ma'aikatan sashen Hausa. Ku huta lafiya.
Allah Ya taimaka.
Naku,
Salisu Muhammad Dawanau