kungiyar masu sauraron rediyon,
Kasar sin ta jihar sokoto,
Nigeria.
A gaskiya ina mai yabawa tare da jinjina ga kasashen duniya musamman kasar sin da sauran manyan kasashen duniya wajen nuna damuwarsu tare da mayar da hankali ga kasashenmu na Afrika, a lokacin da cutar Ebola ta addabi kasashenmu na Afrika inda kasar Sin ta yi kokari kai dauki ga kasashen da abin ya shafa da suka hada da Nigeria, Laberia Saliyo da saurnsu, inda shigar kasar Sin ta taimakama kasashenmu na Afrika baki daya wajen hanzarta dakile cutar mai saurin kisa kamar wutar daji.
Ba shakka kasar Sin da sauran kasashen duniya su ba da gagarumar gudummuwa wajen wannan jan namijin aikin ceto al'umma da a tarwatsewa tare da samarwa kasashenda abin ya shafa da taimako mai yawa domin kawar da wannan cuta ta Ebola, abin da a halin yanzu an bayar da sanarwar kubutar da dukkanin kasashen da ke fama da wannan matsala a nafiyarmu ta Afrika baki daya, muna jinjina ga dukkanin shuwagabannin kasar Sin da ma al'ummar kasar Sin da na duniya baki daya domin wannan jan namijin kokari da suka nunama nafiyamu ta Afrika domin kawar da cutar Ebola a doron kasa baki daya tare da fatar Allah ya bar zumuncin da ke tsakanin Sin da Afrika baki daya, amin.