Kwana biyu ban ji daga gare ku ba shi yasa naga ya dace in aika muku sakon gaisuwa, da kuma fatan alheri musamman a wannan lokaci da muke hango ranar 29 na watan Mayu da Muhammadu Buhari zai dare karagar mulkin kasata Najeriya a wannan rana.
Hakika, mun yi zabe irin wanda ba a taba yi ba a tarihin zabubbukan Najeriya. Kuma muna fatan samun sosai a duk kan fannoni ta yadda kowa zai amfana ba tare da fin karfi ko zalunci ba.
Ina fata zaku kasance cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Naku a kullum,
Salisu Muhammad Dawanau