Zuwa ga sashin Hausa na CRI, da fatan kuna nan lafiya amin. Mun aiko wasikar ne dan mu yaba wa gwamnatin kasar Sin bisa yadda cikin hanzari suka aika da rikunin farko na ma'aikatan agajin gaggawa da kuma kayaiyakin agaji ga al'ummar da masifar girgizar kasa ta ritsa da su a kasar Nepal inda kawo yanzu muke samun labari cewa, akalla mutane 4,00 zuwa 5,000 ne suka rasu yayinda wasu da dama suka jikkata sakamakon abkuwar girgiza kasa a kasar Nepal wadda ta shafi al'ummar sinawa dake jihar Tibet mai cin gashin kanta inda anan ma sinawa akalla 25 ne suka rasu a jihar Tibet ta kasar Sin. Muna mika sakon jajenmu ga al'ummar kasar Sin da al'ummar kasar Nepal da fatan hakan ba zai kara abkuwa ba a kasashen 2 ba(china, Nepal) amin.
Daga masu sauraronku, Alhaji Ali kiraji Gashua Da Alhaji Gambo Ringim mai yankan farce Gashua Da Usman mai wake Gashua, cri Hausa listener's club na jihar Yobe, Nigeria.