A baya, lokacin da nake aika muku da rahotannin sa ido game da shirye-shiryenku na kullum, na san na kan yi nazarin yanayin wasu gidajen rediyo ne kafin in ba ku shawara a kai.
Ina so ku sani cewar akwai wani shiri na DW Hausa mai taken 'Afirka a mako', wadda ke yin sharhi da tsokaci bisa ga abubuwan da suka faru a kasashen Afirka masu nasaba da zuba jari da kasuwanci da yanayi tsaron kasa da kasa, da na zamantakewar al'umma da yawon shakatawa da dai sauransu.
SHAWARA: Kowa ya san karfin kasar Sin da na wasu kasahen da ke Nahiyar Asiya. Ina gani ya kamata ku kirkiro mana da wani sabon shiri mai kama da na DW Hausa din, wanda zai rika kawo mana bayanai na zuba jari da dai wasu muhimman bayanai masu nasaba da wannan kokari na kasar Sin da na sauran kasashen da ke Nahiyar Asiya din.
Muna fata zaku bincika wannan da tunanin basira ta yadda duk mai sauraronku zai amfana.
Naku, Salisu Muhammad Dawanau