Tun a ranar asabar da gwamnatin kasar Nepal suka shelanta wa duniya cewa, girgizar kasa mai karfi ta abka wa kasar Nepal, nake maida hankali a dangane da halin da al'ummar kasar Nepal suke ciki da kuma tunanin da na yi cewa kasar Nepal tana makwabtaka da kasar Sin. Bisa wannan bala'i da ya abku a kasar Nepal wadda kuma ya shafi al'ummar jihar Tibet na kasar Sin inda aka ba da labarin rasuwar a kalla sinawa 20 a jihar Tibet sakamakon girgizar kasar da ta abku a kasar Nepal, muna mika sakonmu na jaje da ta'azziya da alhini ga kasashen Sin da Nepal, da fatan Allah ya kiyaye abkuwar hakan a nan gaba, amin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, shugaban cri Hausa listener's club na jihar Yobe, Nigeria.