in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Allah daya gari Bambam
2015-05-13 08:55:50 cri

Zuwa ga sashin Hausa na Radiyo kasar Sin, da fatan duk kuna nan lafiya, amin. A ranar juma'a 08 ga watan May 2015, na saurari shirinku na 'Allah daya gari Bambam' wanda malamai a cikin shirin suka yi tsokaci adangane da gudumowar da tawagar likitocin kasar Sin suke bayarwa ga al'ummomin wasu kasashe ta fannin kiwon lafiya. Agaskiya jagorar tawagar ma'aikatan jinya na kasar Sin zuwa kasar Cambodia madam Wang ta bani ta'ajibi da mamaki ganin cewa, madam Wang tana da shekaru 56 ta fara tsofa ganin yawan shekarunta, amma ta iya bada gudumowa ta fannin bada aikin jinya ga marasa lafiya masu yawa a kasar Cambodia inda madam Wang da sauran abokan aikinta sinawa suka samu babban yabo daga mahukuntan kasar Cambodia. Yawan yan kasar Cambodia da tawagar likitocin kasar Sin suka basu kulawar masamman ta fannin jinya sun kai akalla 10,000 lamarin da ya ja hankulan yan kasar Cambodia tare da samun babban yabo daga kasashen ketare. Banda wannan kuma, tawagar kasar Sin sun bada babbar gudumowa a kasashen yammacin Afirka inda suka yi fama da cutar ibola inda tasirin ma'aikatan jinya daga kasar Sin ya kai wani mataki na koli, lamarin da ya taimaka wajen kawar da cutar Ibola a kasashen cikin hanzari. Yana da kyau, kasashen duniya su mika yabansu ga gwamnatin kasar Sin bisa gudumowar tawagar likitocin kasar Sin suka bayar ga mutanen da suka harbu da cutar ibola mai saurin kisa. Ta fannin bada aikin jinya a kasashen ketare, likitocin kasar Sin sun yi wa sauran takwarorinsu na wasu kasashen waje zarra da fintinkau wajen nuna kwarewa da kwazon aikin jinya.

Daga mai sauraronku a kullum, Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China