Duk wani mai sha'awar yin huldar cinikaiya da kuma neman karin bayani adangane da hakikanin huldar amunci da diplomasiyya da musayar al'adu tsakanin nahiyar Sin ta zamani da kasashenmu na Afirka masu tasowa, to ya dunga mai hankali sosai ga shirin 'sin da Afirka' wanda madugun shirin malam Bako ke jagoranta a duk mako. A ranar talata 21 ga watan April 2015 da yammaci, na saurari Hirar Malam Bako da wani dan kasuwa da ya zo kasar Sin daga kasar jamhuriyar Niger na samu karin fahimta adangane mu'amular cinikaiya da kasuwanci tsakanin kasar Sin da kasashenmu na Afirka masu tasowa. Banda wannan, ina yaba wa gwamnatin kasar Sin bisa jaddada karin sabuwar huldar masamman ta fuskar tattalin arziki da mu'amula da sabuwar gwamnatin saban shugaban kasar taraiyar Nigeria Gen. Muhammadu Buhari wanda zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin saban shugaban kasar taraiyar Nigeria a 29 ga watan Mayun shekara ta 2015. Ni ma da sauran al'ummar taraiyar Nigeria muna maraba da kalaman shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping na kara kyautata yin hulda da taraiyar Nigeria bisa manyan tsare-tsare da hadin gwiwa cikin lumana. A dogon lokaci ne, kasar Sin ke yin huldar amunci da taraiyar Nigeria da ma sauran kasashenmu na Afirka masu tasowa. Kasar Sin tana sahun koli a dud duniya wajen yaki da cin hanci da rashawa kuma sabuwar gwamnatin Gen. Muhammadu Buhari na daura muhimmanci ga yaki da cin hanci da rashawa a Nigeria, dan haka muna fata gwamnatin kasar Sin za ta yi huldar hadin gwiwa adangane da batun yaki da cin hanci da rashawa da taraiyar Nigeria. Wslm.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.