Bayan gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan alheri ga baki dayan ma'aikatan ku a birnin Beijing, ina kuma fatan duk kuna cikin koshin lafiya. Bayan haka, ina farin cikin shaida mu ku cewa, na samu sauraron shirin ku na kula da lafiyar jiki na baya bayan nan ta hanyar ziyartar shafin ku na yanar gizo.
Hakika, wannan shiri ya yi ma'ana matuka sakamakon yadda ya kawo shawarwari na daukan matakan kariya daga kamuwa da manyan cutuka da ke da alaka da cutar hawan jini, kamar shanyewar rabin jiki ko cutar koda da dai sauransu, ta hanyar kula da kai da kuma ziyartar asibiti akai akai. Babu shakka, cutar hawan jini ta riga ta zamanto kan gaba wajen barazana ga koshin lafiyar mutanen kasa ta Nijeriya musamman wadanda shekarun su na haihuwa ya zarce 40, watakila saboda al'adar mutanen Afirka na rashin bayar da kulawa ga batun motsa jiki yadda ya kamata ga kuma cin abinci akai akai da ke dauke da sinadarin 'carbohydrate' wanda ke narkewa zuwa sukari a jikin mutum.
Alkaluma sun nuna cewa, masu fama da cutar hawan jini suna karuwa a koda yaushe, amma abin takaici al'umma ma fi rinjaye ba sa damuwa da zuwa asibiti ko kuma bibiyar halin da cutar ke ciki a jikin su don daukan matakin da ya dace. Wannan dalili da wasu su ke sa cutar ta samu gindin zama a jikin mutum har ma ta kai matsayin gagara magani ko kuma sai ta riga ta haifar da wata babbar illa sannan za a fara zuwa asibiti.
Dangane da haka, ina kira ga ma su sauraron sashen Hausa na CRI da su nazarci bayanai da kuma shawarwari da ke cikin wannan shiri na Kiwon Lafiya domin fara bayar da shawarwari ga ma su fama da cutar hawan jini da ke cikin kowanne iyali, ta hanyar bayyana mu su irin hadarin da ke tattare da rashin kula da cutar yadda ya kamata. Ta hanyar yin haka, za a samu wayar da kan dimbin al'umma, lamarin da ka iya kawo saukin illar da cutar ke haifarwa idan ta tsananta.
Madalla da kokarin malama Tasalla Yuan da sauran abokan aikinta a sashen Hausa wajen zakulo wannan bayani mai matukar muhimmanci tare da gabatar mana da shi ta hanyar rediyo da kuma shafin yanar gizo na sashen Hausa CRI domin sake saurara ga wadanda suka kuskure sauraron shirin tun da farko. Da fatan za ku ci gaba da kawo mana shiruka masu ma'ana kamar haka a nan gaba. Na gode.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria