Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda na ke lafiya. Bayan haka, ina mai farin cikin sanar da ku cewa na samu sauraron sabon shirin ku na 'Allah daya gari bamban' wanda malamai Lubabatu da Maman Ada suka gabatar mana ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu.
Hakika, wannan shiri ya kayatar dangane da bayanai kan daya daga cikin kananan kabilun kasar Sin wato kabilar Uyghur. Abin mamaki dangane da wannan shiri shi ne, na dade ina jin labarin wannan kabila ta Uyghur musamman yadda jihar Xinjiang da kabilar ta Uyghur ke da rinjaye ta shahara, amma duk da wannan suna da farin jini da kabilar Uyghur ke da shi yawan su bai fi dubu 13 da 'yan wasu daruruwa ba. Ba shakka, kabilar Uyghur ta yi fice wajen al'adun ta masu ban sha'awa da suka hada da tufafi masu launi da ke jan hankali da wake wake game da raye raye masu nishadantarwa. Wani abin burgewa da kabilar ta Uyghur shi ne yadda Allah SWT Ya albarkace su da maka makan filayen ciyayi a ko'ina, lamarin da ya ba su damar mallakar albarkatun dabbobi, 'yayan itatuwa iri iri da dai sauransu.
Amma duk da irin wannan baiwa da kabilar ta Uyghur ke da shi, abin takaici shi ne yaren na Uyghur da ke tattare da dorewar kyawawan al'adun su na fuskantar barazanar bacewa sakamakon rashin nuna sha'awar koya daga bangare matasa, game da wahalar koyo na shi kansa yaren. Dangane da haka, ya dace gwamnatin kasar Sin ta bullo da sababbin manufofi da za su kai dauki ga kyawawan al'adun kananan kasar Sin ba ma kawai kabilar ta Uyghur ba. Hakika, sauye sauyen da zamani ya haifar sun kawo nakasu ga wanzuwar wasu al'adun gargajiya masu daraja musamman al'adun da ba na kaya ba.
Wata hanya mai sauki da za a iya cusa riko da al'ada tsakanin matasa shi ne, gindaya sharadin cewa, duk wani matashi ko matashiya ba za ta ko zai samu shiga jami'a ba ko samun aikin gwamnati sai ya ko ta iya yaren su na gargajiya. Domin yin haka zai taimaka wa matasa da su yi riko al'adun su ko da kuwa sun samu kansu cikin manyan biranen kasar Sin da ke da ci gaban zamani.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria