in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har kullum ina tare da cri Hausa
2015-04-20 15:39:15 cri

A matsayina na mataimakin shugaban cri Hausa listener's club na jihar Yobe, ina mai yaba wa ma'aikatan sashen Hausa na cri bisa kokarinsu na fahimtar da mu masu sauraro hakikanin yadda kasashen Sin da Nigeria da ma daukacin kasashen nahiyar Afirka ke yin hulda da juna a dogon lokaci. Wannan gidan Radio, yana kara kyautata mu'amularsa da mu masu sauraro inda gidan Radio ke shirya gasar kacici-kacici ta masamman dan karin fahimtar kasar Sin ga mu masu sauraro ga kuma wata kyakkyawar gasa dake gudana adangane da abuncin halal na al'ummar musulmi dake da rinjaye a jihohin Ningxia da Xi'an. Hakika wannan gasa adangane da abuncin halal a kasar Sin, ya taimaka wajen karin wayin kai ga milyoyin masu sauraro adangane da yanayin rayuwar musulmi a kasar Sin. Bayan haka, ina bada shawara ga cri Hausa da su taimaka su wallafa ritattafan koyon harshen Sinanci dan aika wa mu masu sauraro dake sha'awar koyon sinanci. Domun da yawa daga cikin masu sauraro muna da sha'awar koyon sinanci kuma wallafa littafin koyon sinanci zai taimaka sosai wajen fahimtar harshen sinanci.

Daga mai sauraronku a kullum, Usman mai wake Gashua, mataimakin shugaban cri Hausa listener's club na jihar Yobe, Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China