Cikin alhini da tausayi, ina mika sakon jaje da ta'azziya ga al'ummar kasar Sin bisa harin da wasu mahara dake dauke da wukake suka kai akan dalibai a wata college dake birnin Kunming dake lardin Yunnan a sashin kudu maso yammacin kasar Sin, lamarin da ya sabbaba rasuwar dalibi daya yayinda wasu daliban su 5 suka jikkata a ranar alhamis 12 ga watan Maris 2015. Kana ina mika sakon jaje da ta'azziya ga gwamnatin kasar Sin da al'ummar kasar Sin, bisa rasuwar sinawa 4 yayinda wasu karin sinawa 4 suka jikkata a sa'ilin da wata motar Taxi ta yi karo da wata mota karama inda nan take motar ta kama da wuta, lamarin da ya haddasa rasuwar sinawa su 4 yayinda wasu mutane 4 suka jikkata a garin Jining dake lardin Shandon dake sashin gabashin kasar Sin.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, Nijeriya