in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Me ka sani game da sashen hausa na cri
2015-02-20 15:05:30 cri
Ba shakka na san sashen hausa tun shekarrau fiye da talatin da suka gabata kuma a ko da yaushe ina alfahari da sashen hausa na cri kuma ina bugun gaba da shi sashen hausa na cri,tare da alfahari da dukkanin shiraruwansa masu farin jini tare da bayar da illimin tarwa tare da nishadantarwa ga dukkanin masu sauraronsa, haka ina alfahari da dukkanin kwararrun ma'aikatansa tare da jin dadin yadda suke gudanar da ayukansu baki daya.

Har wa yau sashen hausa wata kafa ce mai samar da labaru tare da sanar da mai sauraronsu irin wainar da ke faruwa a fadin duniya, musammamman kasashenmu na afrika, turai, asiya, amurka da ma sauran sassan duniya baki daya. Sashen hausa na cri ya zamo wata kafa ta sada zumunta tsakanin sin da kasashen duniya tare da samar da labarun irin abubuwan da ke faruwa a kasar sin domin masu sauraron tare da bayar da dama ga dukkanin mai sauraro da ma masu kallon tashar cri ya san kasar sin tare da manufofin kasar sin zuwa ga kasashen duniya musammam yankin kasashen afrika da ma duniya baki daya.

Har wa yau cri hausa suna kokarin samar da wata kafa ta sada al'adun kasar sin da na nafiyarmu ta afrika tare da sanar da al'ummar afrika wajen irin taimakon da sin ke aiwatarwa tsakanin sin da nafiyarmu ta afrika, idan muka dubi sashen hausa na cri yana gabatar mana da shiraruwa masu muhinmanci tare da fadakarwa ga dukkani masu sauraronsu, misali idan muka dubi irin rawar da sashen hausa na cri ya taka wajen wayarma masu sauraronsa da kansu akan muguyar cutar nan ta ebola da ta addabi kashenmu na afrika, to a gaskiya sashen hausa ya ba da gagarumar gudunmuwa wajen fadakar da jama'a a kan kare kai tare da sanarda al'ummar duniya irin taimakon da kasar sin ke bayarwa domin kawar da cutar ebola a kasashenmu na afrika, ba shakka sashen hausa na cri ya bayar da gagarumar gudunmuwa ta wannan fanni.

Ba shakka wadannan ma'aikata da suka yi zance a cikin wannan faifan bidiyo na cri ba shakka kwarranru ne kuma suna bayar da gudunmuwa mai muhimmanci ga samar da labaru da doron sashen hausa na cri , ba shakka ni a matsayina na mai sauraron cri ina alfahari da sashen hausa na cri da ma dukkani ma'aikatansa baki daya.

Wassalan ni ne mai sauraronku a ko da yaushe,

SHUGABA BELLO ABUBAKAR MALAM GERO,

KUNGIYAR MASU SAURARON SASHEN HAUSA NA CRI,

TA JIHAR SOKOTO ,

NIGERIA.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China