Bayan wannan, ina so in tunatar da mu cewa 'yau da gobe sai Ubangiji' domin yau kusan shekaru biyu da rabi kenan rabona da kasar Sin bayan ziyara da muka yi tare da wasu masu sauraron CRI daga kasashe daban-daban.
Daga Beijing, muka je Jihar Xinjiang, muka kekkewaya wannan jiha mai cin gashin kai da albarka, kasancewar jiha ce mai dauke da kananan kabilu masu yawan gaske, da yanayi mai ni'ima da zaman lumana babu tsangwama. Ga na'ukan abinci da kayan marmari iri-iri, ga albarkatun noma masu inganci, kuma jiha ce mai filayen ciyayi da ake kiwon dabbobi kanana da manya don ci da sayarwa da samun kudin shiga. Kana,galibin Musulman kasar Sin suna wannan jiha.
A wannan ziyara tamu, mun samu karin ilimi da fahimta na zamantakewar Sinawa daki-daki, mun yi mu'amala da al'ummar da muka da su a can, sannan an karrama mu fiye da misali. Wannan ya sa mun ga yadda ake nuna yakana da karimci ga bako a kasar Sin. Mun yi murna sosai kasancewar ziyarar ta bamu damar haduwa da sabbin abokai, da karin ilimi da fahimta da sauransu.
A karshe, ina fata sauran masu sauraron CRI su ma zasu samu irin wannan dama na kai ziyara Sin. Da fatan Allah Ya taimakemu baki daya.
Ku huta lafiya. Naku,
Salisu Muhammad Dawanau