Tare da fatan baki dayan ma'aikatan ku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda na ke lafiya. Bayan haka, tun bayan da aka bude taruka biyu na majalisar wakilan jama'a da ta bayar da shawara kan harkokin siyasa a farkon watan nan na Maris na ke ta bibiyar al'amuran da ke gudana a tarukan na bana.
Amma a zahirin gaskiya, batutuwa biyu sun fi jan hankali na sakamakon tasirin su ga rayuwar yau da kullum, wato batun gurbatar muhalli da batun daidaituwar kudaden shiga na al'umma. Da farko dai, na fahimce cewa batun na muhalli na cikin na gaba gaba a wajen taron sakamakon yin la'akari da barazanar da gurbatar iska ke kawowa kasar Sin ta fannoni da dama. A nan, ya zama wajibi a yaba wa shugabannin na kasar Sin dangane da yadda suka daura damarar yaki da gurbatar iska a manyan biranen kasar. Saboda mazauna na biranen su samu tsira daga cutukan da suka shafi numfashi ko sankarar huhu, da sauransu. A daya hannun kuma, kyautatuwar yanayin iska zai kara jan hankali baki daga kasashen ketare don yawon shakatawa.
Sai batun daidaita kudaden shiga na al'ummar Sinawa, wannan shi ma yana da muhimmancin gaske bisa la'akari da yadda darajar biranen kasar Sin ke dagawa. A duk lokacin da a ke samun bunkasuwa to darajar rayuwa ita ma tana karuwa, karuwar darajar rayuwa na tafiya kafada da kafada da karuwar kudaden shiga na al'umma.
Dangane da haka, ina yin kyakkyawan fatan alheri da nasara kan batutuwan da za a tattauna a yayin tarukan biyu na bana. Tare da fatan za a samu nasarar aiwatar da baki dayan shawarwarin da a ka cimma a taron wanda zai haifar da sakamako da tasiri mai nagarta ga rayuwar al'umma Sinawa da kuma alakar kasar ta Sin da sauran kasashen duniya.
Na gode.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo,
Nigeria