Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ina farin cikin shaida mu ku cewa, ranar 25 ga watan Fabrairu na saurari maimaicin shirin 'Gani Ya Kori Ji' wanda malamai Ibrahim Yaya da Maman Ada suka tattauna da shugaban sashen Hausa malam Sanusi Chen dangane da al'adun bikin bazara.
Hakika, bikin bazara na tattare da abubuwa masu ban sha'awa da kayatarwa sosai, ban da wasan wuta mai jan hankali da ke alamanta shigowar sabuwar shekara, abinci iri daban daban da Sinawa kan tanada yayin bikin tare da cin abincin tare da iyali baki daya al'ada ce mai ban sha'awar gaske. Wani abu da ke jan hakali na dangane da bikin bazara shi ne, yadda miliyoyin Sinawa ke kwarara daga wani sashe na kasar Sin zuwa wani sashe duk a kokarin da suke na komawa gida don gudanar da wannan biki tare da iyalansu.
Amma a hakika, wasan wuta ya fi jan hanakli na cikin dukkan wasannin da shagulgulan bikin bazara na Sinawa sakamakon yadda sararin samaniya ke daukan haske da tartsatsin wuta mai launi iri iri, wato lamarin dai sai wanda ya gani. Ban da wasan wuta kuma, wani abu daban da ke ban sha'awa yayin bikin bazara shi ne, yadda manyan birane kamar Beijing da ke fuskantar matsalar cunkoson mutane da na ababen hawa kan samu sararawa ta 'yan makonni, sakamakon ficewar baki 'yan cirani zuwa garuruwan su don halattar bikin na bazara. Lamarin da kan bayar da dama ga mazauna birnin na dindindin su samu dan sararawa.
Ina fatan al'ummar Sinawa za su gudanar tare da kammala wannan biki na sallar bazara mai alamar tinkiya cikin zaman lafiya, kwanciyar hankali da walwala.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Chiromawa Quarters
P.O. Box 1147
Kano State 700001
Nigeria