A hakika dai, yayinda al'ummar kasar Sin ke maida hankali ga muhimmin mashahurin bukukuwan bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin ke gab da zuwa, ina mai nuna sha'awata tare da maida hankali adangane da wannan shekara ta bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Dud da cewa dukkan al'ummar kasar Sin suna da zumudin zuwan wannan biki na bazara, amma a bana bikin ya ja hankali sosai fiye ma da na lokutan shekarun da suka gabata, bisa la'akari da cewa tun gabannin ranar bukukuwan shugaban kasar Sin mr. Xi Jinping ya koma kauyensu inda ya taba aiki dan shi ma a yi bikin bazara da shi. Kana yadda sinawa ke ci gaba da yin tururuwa tare da yin rigegeniya zuwa kauyukansu dan taya juna murna da farin cikin bikin bazara na kalandar gargajiya ta kasar Sin. Agaskiya bukukuwa irin wannan da al'ummar kasar Sin ke yi duk shekara, yana jan hankalina kuma yana burgeni sosai kuma hakan zai kara janyo hankulan masu zuwa ziyara da yawan shakatawa da bude idanu a kasar Sin ganin yadda gwamnatin kasar Sin da al'ummar kasar Sin ke kara kayatar da bikin duk shekara tare da martaba bikin na bazara dan kyautata jin dadin sinawa dake gudanar da shagulgulan bikin a kowace shekara. Ina fata sashin Hausa na cri za ku maida hankali ga wannan muhimmin biki dan kawo mana labaru da rahotanni da za su kara wayin kai da karin fahimtar bikin bazara bisa kalandar gargajiya na kasar Sin ga mu masu sauraro. Wslm.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.