logo

HAUSA

Motsa jiki yana magance cutar sankarar hanta

2022-02-23 07:59:42 CRI

Motsa jiki yana magance cutar sankarar hanta_fororder_src=http___pic.51yuansu.com_pic3_cover_02_89_22_5ab374fb76dbf_610&refer=http___pic.51yuansu(1)

Rahoton binciken da masanan kasar Austriliya suka gudanar ya nuna cewa, motsa jiki yana taimakawa wajen dakile cutar sankarar hanta.

Binciken, wanda jami’ar kasar Australiya, wato Australian National University (ANU) ta wallafa a kwanakin baya, ya gano cewa, motsa jiki yana taimakawa wajen samar da riga-kafin hana kamuwa da cutar sankarar hanta a mataki na farko-farko ga beraye.

An kiyasta cutar sankarar hanta ta kashe mutane 2,161 a kasar Australia a shekarar 2019. A cewar kwamitin yaki da cutar sankara na kasar Australiya, yawan mutanen da suka rayu fiye da shekaru 5 bayan da aka yi musu jinyar cutar sankarar hanta ya kai kashi 18 bisa 100, adadin da ya kusan yi daidai da yawan mutanen da suka rayu fiye da shekaru 5 bayan da aka yi musu jinyar cutar sankarar huhu.

Geoff Farrell, mawallafin binicken na jami’ar ANU, ya bayyana cewa, sakamakon binciken zai yi tasiri kai tsaye ga wadanda suke fuskantar barazanar kamuwa da cutar sankarar hanta.

A bayanin da ya yi a wani taron manema labaru ya bayyana cewa, binciken ya nuna cewa, motsa jiki zai iya samar da cikakkiyar kariya a matakin farko ga mutanen dake da barazanar kamuwa da cutar sankarar hanta.

A cikin binciken, masu nazarin sun mayar da hankali wajen bayyana muhimmiyar alakar dake tsakanin cutar sankarar hanta da cutar samun kiba sosai a kewayen hanta sakamakon matsalar kiba da ciwon sukari mai nau’i na 2.

An raba beraye masu matukar nauyi dake fama da cutar samun kiba sosai a kewayen hanta zuwa rukunoni biyu, rukuni na farko suna yin motsa jiki a ko da yaushe, yayin da dayan rukunin ba sa motsa jiki.

Masu nazarin sun gano cewa, motsa jikin yana rage tsananin cutar samun kiba sosai a kewayen hanta.

Farrell ya yi nuni da cewa, “Mun riga mun sani cewa, motsa jiki yana taimakawa wajen rage adadin nau’ikan cututtukan sankara, to sai dai, muna son mu gano ko motsa jikin zai iya rage adadin cutar sankarar hanta."

A cewarsa, “kusan dukkan berayen da ba sa motsa jiki sun kamu da cutar sankara a cikin watanni shidda. Daga cikin berayen dake motsa jiki, babu wanda ya kamu da cutar sankarar hanta a cikin watanni shidda, hakan ya nuna cewa, motsa jiki yana yin kandagarkin kamuwa da cutar sankarar hanta tun a matakin farko."

Ya kara da cewa, yanzu akwai kwararan hujjoji dake nuna cewa, motsa jiki zai iya taimakawa, musamman ga mutane masu tsananin kiba da suke fama da cutar sukari mai nau’i na 2. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan