logo

HAUSA

Rashin motsa jiki yana haifar da karuwar kamuwa da ciwon sankara

2021-04-04 20:30:38 CRI

Rashin motsa jiki yana haifar da karuwar kamuwa da ciwon sankara_fororder_dd

Mujallar kwalejin nazarin ciwon sankara na kasar Amurka da aka wallafa a kwanan baya ta kaddamar da rahoton shekara-shekara dangane da ciwon sankara a kasar ta Amurka, inda aka nuna cewa, daga shekarar 1999 zuwa 2016, jimillar mutanen da suka mutu sakamakon ciwon sankara tana ci gaba da raguwa a Amurka, duk da haka a shekarun da suka gabata, yawan masu kamuwa da ciwon sankara sakamakon rashin motsa jiki da kuma yadda masu kibin da ya wuce kimi a Amurka yake ta karuwa.

Kwalejin nazarin ciwon sankara na kasar Amurka, cibiyar kandagarki da dakile cututtuka ta kasar Amurka, kungiyar ilmin ciwon sankara ta kasar Amurka da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, sun kaddamar da wannan rahoto ne cikin hadin gwiwa, inda aka nuna cewa, sakamakon raguwar yawan masu shan taba cikin dogon lokaci a kasar ta Amurka, ya sa yawan masu fama da ciwon sankarar huhu, mara da makogwaro yana ta raguwa. Amma a ‘yan shekarun baya da suka wuce, yawan masu fama da ciwon sankarar mahaifa, mama bayan da mata suka daina al’ada , da uwar hanji tsakanin matasa yana ci gaba da karuwa, wadanda aka kamu da su saboda fama da matsalar karancin matsa jiki, da kuma kibar da ta wuce kima.

Har ila yau kuma, rahoton ya yi nazari kan bambancin da ke tsakanin mata da maza a fannin kamuwa da ciwon sankara a kasar Amurka. Galibi dai yawan maza masu kamuwa da ciwon sankara ya fi na mata yawa. Amma a cikin Amurkawan da shekarunsu suka wuce 20 amma ba su kai 50 da haihuwa ba, yawan mata masu fama da ciwon sankara da kuma yawan wadanda ke mutuwa sun fi maza yawa.

Rahoton ya yi karin bayani da cewa, a cikin Amurkawan da shekarunsu suka wuce 20 amma ba su kai 50 da haihuwa ba, mata sun fi kamuwa da ciwon sankarar mama, da gujiyar wuya, da kuma ciwon sankarar tantanin halitta, yayin da maza su kan yi fama da ciwon sankarar uwar hanji, golo da ciwon sankarar melanoma. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan