Yin abubuwan da ke cikin takardar jerin abubuwan da ake fatan yi a sabuwar shekara yana taimaka wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sankara
2020-11-29 19:22:39 CRI
Yanzu sabuwar shekarar 2021 tana kan hanya. Masu karatu, ko kun rubuta takardar jerin abubuwan da kuke fatan yi a sabuwar shekara domin kasancewa cikin koshin lafiya? Masu ilmin kimiyya na kasar Birtaniya sun ba mu shawarar cewa, zai fi kyau a yi kokarin yin wadannan abubuwan da ke cikin takardar a sabuwar shekara, saboda zaman rayuwa ta hanyar da ta dace yana rage barazanar kamuwa da ciwon sankara har kashi 1 cikin kashi 3.
Masu nazari daga jami’ar Cardiff ta kasar Birtaniya sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a kwanakin baya, inda suka yi bayani da cewa, sun tantance bayanan mutane kimanin dubu 500 da aka tanada cikin bankin halittu na Birtaniya, sun takaita hanyoyin da ake bi wajen yin rayuwa yadda ya kamata, alal misali, rashin shan taba, tabbatar da daidaiton nauyin jiki, motsa jiki a kai a kai, cin abinci ta hanyar da ta dace, kayyade yawan giyar da ake sha da dai sauransu. Masu nazarin kuma sun kimanta alakar da ke tsakanin wadannan hanyoyi da kuma barazanar kamuwa da ciwon sankara cikin tsawon shekaru.
Masu nazarin sun gano cewa, wadannan kyawawan hanyoyin rayuwa suna rage barazanar kamuwa da ciwon sankara da kashi 1 cikin kashi 3 baki daya, suna kuma rage yawan mutuwar mutane sakamakon ciwon sankara. Ko wace kyakkyawar hanyar rayuwa tana rage barazanar kamuwa da ciwon sankara da kashi 8 cikin kashi 100.
Sakamakon nazarin ba ya wuce zaton mutane. Sanin kowa ne cewa, yin rayuwa ta hanyar da ta dace yana taimakawa wajen kiwon lafiyar mutane. Duk da haka wannan nazari ya nuna mana hakikanin alkaluma na raguwar barazanar kamuwa da ciwon sankara sakamakon yin rayuwa ta hanyar da ta dace.
Masu nazarin sun yi bayanin cewa, watakila abin da ya fi dacewa yawancin mutane su yi shi ne, tsayawa tsayin daka kan wata kyakkyawar hanyar rayuwa a ko da yaushe. Ba a bukatar bin wadannan kyawawan hanyoyin rayuwa da muka ambata a baya duka.
Dangane da wannan nazari, madam Zhang Chuji, wata likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi karin bayani da cewa, hakika dai, baya ga rage barazanar kamuwa da ciwon sankara, yin rayuwa ta hanyar da ta dace yana da amfani a wasu fannoni. Bai haifar da illa, kuma ba a bukatar kashe kudi. Watakila abu daya tilo mai wuyar yi shi ne tsayawa kan yin rayuwa ta hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)