logo

HAUSA

Mahaifar mata masu juna biyu da suka kamu da COVID-19 sun nuna rauni

2022-01-19 10:40:08 CRI

Mahaifar mata masu juna biyu da suka kamu da COVID-19 sun nuna rauni_fororder_src=http___img.toumeiw.cn_upload_images_20201110_a8705ebd3e43e4f78a8743807748298a&refer=http___img.toumeiw(1)

Sakamakon bincike da asibitin kula da mata na Northwestern na kasar Amurka ya gudanar kan mahaifar mata 16 da aka tabbatar sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19, yayin da suke da juna biyu sun nuna alamun rauni, bayan da suka haihu.

Matan 16 da aka gudanar da bincike a kansu, sun haifi jariransu a asibitin kula da mata na Northwestern Medicine Prentice. Mata hudu sun zo da alamun mura kamar makonni uku zuwa biyar kafin su haihu, kuma sakamakon gwaje-gwaje sun nuna cewa, sun kamu da kwayar cutar. Sauran mata duka sun kamu da cutar, a lokacin da suka zo haihuwa. Wasu biyar kuma ba su taba nuna alamun cutur ba, yayin da sauran mata duk suka kasance da alamun cutur a lokacin da suka zo haihuwa.

A cewar Emily Miller, mataimakiyar farfesa a fannin likitan mata a makarantar ilmin likitanci ta NU Feinberg, likitar mahaifa ta asibitin Northwestern, kana daya daga cikin likitocin da suka wallafa wannan rahoto, jariran suna da koshin lafiya, kuma ba su da wata tawaya, amma binciken mu ya nuna cewa, jini ba ya kwarara da yawa kuma yawancin mahaifar, sun kankance matuka. Haka kuma mahaifar kamar ba sa wani amfani. Ko da rabinta yana aiki, yawancin jariran suna da lafiya sosai. Duk da haka, yayin da yawancin jariran suna da koshin lafiya, akwai hadarin cewa, wasu masu dauke da juna biyu za su iya gamuwa da lahani."

Mahaifa ita ce gaba ta farko da ake fara samu wajen raya dan tayi. Tana aiki ne a matsayin huhun dan tayin, da hanji, da koda da hanta, Tana kuma daukar iskar oxygen da abubuwan gina jiki daga magudanar jinin uwa da musayar abubuwan da jiki ya gama amfani da shi.

Mahaifa tana aiki ne kamar na'urar dake taimakawa yin numfashi ga dan tayi, kuma idan ta lalace, za a iya samun mummunan sakamako, a cewar Miller. A cikin wannan takaitaccen bincike, sakamakon binciken ya samar da wasu alamomin dake nuna cewa, na'urar ba za ta iya yin aiki sosai kamar yadda ake so ba, idan mahaifiyar ta kamu da cutar ta COVID-19.

Babban marubuci Jeffrey Goldstein, kana mataimakin farfesa a fannin ilimin cututtuka a makarantar nazarin magunguna ta NU Feinberg kuma masanin ilimin likitanci a asibitin NorthWestern, ya bayyana cewa, akwai matsalar gudanar jini a jijiyoyin masu fama da COVID-19, kuma bincikenmu ya nuna mana cewa, akwai wani abu da ke haifar da daskarewar jini a jikunan masu fama da annobar COVID-19, kuma hakan yana faruwa a cikin mahaifa. (Ibrahim)

Ibrahim Yaya