logo

HAUSA

Yu Jing: Telar Karfe dake dukufa wajen aikin kera jiragen kasa

2022-01-10 14:34:28 CRI

Yu Jing: Telar Karfe dake dukufa wajen aikin kera jiragen kasa_fororder_Yu Jing3

Sinawa na kiran Kamfanin CRRC Dalian, mai kera jiragen kasa a matsayin gidan jiragen kasa na kasar Sin. Yu Jing ta kasance mace daya tilo a kamfanin dake da kwarewa a aikin walda. Ta shafe shekaru kusan 30 tana aiki a kamfanin. Mijinta Yang Bo, shi ma mai aikin walda ne a kamfanin na CRRC Dalian, dake lardin Liaoning na arewa maso gabashin kasar Sin. Ma’auratan na zaune ne tare da ‘yarsu daya Yang Yurou da mahaifiyar Yang Bo mai suna Liu Shuyan. Iyalin mai kunshe da mutane 4, na rayuwa cikin jin dadi, kana suna da kirki da kuma son jama’a.

A lokacin da Yu Jing take karama, tana muradin zama tela. “ina mafarkin dinka tufafi masu kyau a duniya a lokacin da nake karama,” cewar Yu. Sai dai, Yu ta sauya ra’ayinta a lokacin da ta nemi gurbin karatu a makarantar koyon sana’o’in hannu bayan ta kammala karatun sakandare. Ta ce, “Mahaifina ya fada min cewa, ‘kina son abubuwa masu kyau ko? Wutar dake fitowa lokacin da ake walda ma tana da kyau.’ Na samu kwarin gwiwa ne daga kalaman mahaifina.” 

A shekarar 1991, Yu Jing mai kusan shekaru 20 da haihuwa ta gama karatu daga makarantar koyon fasahohin kera jiragen kasa na Dalian. Daga baya kuma an ba ta aikin walda a kamfanin CRRC Dalian. Tun daga wancan lokaci, Yu Jing ta kasance wata tela ta musamman, wadda ta mai da karfe a matsayin yadi, injin walda kuwa a matsayin allura da zare.

A matsayin sabuwar shiga, aikin ya zamewa Yu Jing kalubale kuma a ko da yaushe, wurin cike yake da tarsatsin wuta da kura. Yu Jing ta karbi wannan kalubale, kuma ta kuduri niyyar shawo kansu. Ta yi karance-karancen littattafai kan dabarun walda domin inganta fahimta da kwarewarta a fannin. Ta koyi yadda ake aikin daga mataki zuwa mataki daga wajen shugabanta. Yu Jing ta tattara dukkan ayyukan walda da shugabanta ya shirya domin halartar gasar masu aikin walda. Inda ta yi amfani da su a kai-a kai wajen inganta kwarewarta a aikin. Yu Jing ta kan rubuta dukkan abubuwan da ta koya. Ba makawa, ta sha kona hannunta a lokacin da take koyon walda. A ko da yaushe, idan Yu Jing na kammala aikin walda, ta kan bi sannu a hankali, kamar mai aikin zane.

Bisa la’akari da yadda take mayar da hankali kan aikinta, Yu Jing ta inganta kwarewarta sosai. Ta fara koyar da dalibai da jagorantarsu wajen halartar gasanni. Ta kan karfafa musu gwiwa su ci gaba da kirkiro sabbin dabaru. Yu Jing na fatan koyar da dukkan dabaru da gogewarta ga matasa.

Abokan aikin Yu Jing, wadda ta samu nasarori a fannin walda da maza ne suka mamaye, kan kira ta da “telar karfe” . Ta samu lambobin yabo da na karramawa da dama, ciki har da na mace mafi fice a duk fadin kasar Sin. Ta kuma kasance wakiliya yayin tarokaro na 19 na wakilan mambobin JKS.

Yu Jing: Telar Karfe dake dukufa wajen aikin kera jiragen kasa_fororder_Yu Jing1

Yang Bo ya fara aiki da kamfanin CRRC Dalian ne shekaru kalilan kafin matarsa. Ya zama mai aikin walda a kamfanin ne a shekarar 1985. Ya yi aiki tukuru a kamfanin tsawon shekaru 30. Zabar aiki iri daya ya ba ma’auratan wata dama, wanda ke nufin suna da gogewa da dabarun da za su koyawa juna. Yu Jing da Yang Bo, kan tattauna kan dabarun aiki kuma suna koyon abubuwa daga juna domin inganta kwarewarsu da samun nasarori. Idan ana zancen nasarorin da ta samu, Yu Jing kan alakanta hakan da irin tattaunawar da take yi da mai gidanta.

A wasu lokuta, abokan Yang Bo kan tsokane sa cewa, “Yang Bo, matarka ta samu lambobin yabo da na karramawa da dama. Mene ne matsayinka a gidanka?” Yang Bo kan amsa da cewa, “ta bada gagarumar gudunmuwa ga ci gaban kamfaninmu da ci gaban dabarun dake da alaka da jiragen kasa. Ita ce abun alfaharin iyalinmu. Muna kulawa da rayuwa da ayyukan juna. Ina taya ta farin ciki, da iyalinmu. Ban damu da wanda ya fi matsayi ba.”

Mahaifiyar Yang Bo, wato Liu Shuyan ma’aikaciyar kamfanin sufuri ce mai ritaya. Yu Jing na zaune tare da surukarta sama da shekaru 20, tun da ta auri Yang Bo. Yu Jing ba ta taba samu matsala da surukarta ba. A nata bangaren, Liu na alfahari da surukarta, wadda ke ci gaba da kokarin samun sabbin nasarori a aikinta.

Iyalin mai mutane 4, na son zama tare su yi hira. Yu Jing da Yang Bo kan tattauna game da ayyukansu a kamfani. Diyarsu Yang Yurou, ta kan bada labarin rayuwarta a makaranta. Liu kuma kan tuna da abubuwan da suka faru a baya. Saboda irin wadannan hirarraki, iyalin ke da kusanci da juna kuma suke zaune lafiya.

Yu Jing na sane cewa, iyaye na tasiri kan ci gaban ‘ya’yansu. Duk da cewa ta samu lambobin yabo da dama, ba ta taba kasa a gwiwa wajen zage domin cimma manyan burika ba.

A lokacin da diyarta ke shirin jarrabawar shiga babbar sakandare, Yu Jing ta shirya gasa tsakaninta da diyarta. Burin Yang Yurou shi ne, shiga babbar makaranta mai kyau. Burin Yu Jing kuma shi ne, samun babbar shaidar zama mai walda.

Don haka suka fara gasa a tsakaninsu, a daya bangaren kuma suna karfafawa juna gwiwar cimma burinsu. Dukkansu dai, sun samu damar cimma burinsu. Yurou ta shiga makaranta mai kyau, inda daga nan ta samu nasarar ci gaba da karatu a matsayin daliba a fannin ilimin Physics a jami’ar koyar da malaman koyarwa ta Liaoning. Yayin da kuma Yu Jing ta samu babbar shaidar zama mai walda, kuma mace daya tilo dake wannan aiki a kamfannin CRRC Dalian.

Yu Jing: Telar Karfe dake dukufa wajen aikin kera jiragen kasa_fororder_Yu Jing2

A watan Oktoban 2017, Yu Jing ta tafi Beijing domin halartar taro karo na 19 na wakilan mambobin JKS a matsayin wakiliya. Surukarta ta tunatar da ita game da sauke nauyin dake wuyanta a matsayin wakiliyar mambobin jam’iyyar da suka aminta da ita.

Yu Jing ta ce, “kafin a zabe ni a matsayin wakiliya a taron, ina ganin kaina ne a matsayin mai walda kadai, wadda ke bukatar mayar da hankali kan inganta aikinta. Amma bayan na zama wakiliya, na fahimci cewa dole ne in tabbatar da karin mutane sun gaji dabaru da basirarta. A ganina, aiwatar da abun da na koya daga taron na nufin, dole in taimaka wajen samar da wani ayarin matasa masu basira, wadanda suka mallaki ilimin walda da dabarunta da kuma kirkire-kirkire.’’

Yu Jing ba ta taba daukar kanta a matsayin mafi kwarewa a aikin ba, sai dai ta yi ammana cewa ita mai mayar da hankali ce kan aikinta iyakar rayuwarta. Tana kuma farin cikin ganin iyalinta na mara mata baya, a ko da yaushe.

Kande