Amurka Wadda Ta Kashe Wadanda Ba Su Ji Ba Ba Su Gani Ba Ba Ta Da Matsayin Zargin Wasu Kan Hakkin Dan Adam
2021-12-23 21:02:16 CRI
Azmat Khan, wakiliyar jaridar New York Times ta kasar Amurka, ta bayyana cikin dogon bayaninta a kwanan baya cewa, abubuwan da sojojin Amurka suka yi a fagen yakin Gabas ta Tsakiya, ba kura-kurai ne masu ban tausayi ba, domin babu wanda aka yanke masa hukunci, duk da ba su gano fararen hula ba, ba su yi bincike a wurare ba, ba su san dalili ba, ba su kuma koyi darasi ba, kana ba a gano abubuwa marasa dacewa da aka yi ba.
A cikin bayaninta, Azmat Khan ta yi karin bayani, kan yadda sojojin Amurka suka kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba cikin yake-yake, tare da nuna cewa, Amurka ta kirkiro wani tsarin boye ainihin yawan mutuwar mutanen da suka rasa rayukansu a yayin hare-haren sama da gangan, da kuma kara sanya hare-haren sama su dace da doka.
Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, a cikin shekaru 20 da suka wuce, a kasashen Iraki, Afghanistan, Syria da Yemen, sojojin Amurka sun kai hare-haren sama har fiye da sau dubu 90, wadanda suka halaka fararen hula a kalla dubu 48. Sojojin Amurka sun kashe manoman da suke yin girbin hatsi a gonaki, da kananan yaran da suke wasa a titi, da iyalan da suka boye kansu cikin yake-yake da dai sauransu. Wadannan laifufuka masu ban tsoro sun karyata ikirarin Amurka, na cewa wai hare-haren sama ba su halaka fararen hula masu yawa ba.
Amma ya zuwa yanzu, fadar White House ta Amurka ba ta ce komai ba. Bill Urban, kakakin hedkwatar tsakiyar rundunar sojan Amurka ya ce, ana yin kuskure ne duk da amfani da fasaha mafi dacewa da zamani a duniya. Ya ce muna kokarin koyon darasi daga wadannan kura-kurai.
Fararen hula nawa ne sojojin Amurka suka kashe? Iyalai nawa ne suka rabu sakamakon Amurka? Abubuwa masu ban tausayi nawa ne za su sake faruwa a Gabas ta Tsakiya? Sojojin Amurka sun ayyana su a matsayin kura-kurai. Ko wannan shi ne yadda gwamnatin Amurka take kiyaye hakkin dan Adam?
Kamar yadda rahoton kwamitin nazarin hakkin dan Adam na kasar Sin ya fallasa gazawa, da koma baya na demokuradiyyar Amurka, tarihi ya nuna mana cewa, yadda Amurka take wanzar da demokuradiyya a wasu kasashe, bai kawo wa mazauna wurin wadata da ci gaba ba, maimakon haka ya kawo musu sabon bala’in jin kai. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Yunkurin Amurka Na Dakile Ci Gaban Kasar Sin Bisa Hujjar Xinjiang Ba Zai Yi Nasara Ba
- Zhao Lijian: Gwamnatin Amurka ta yi watsi da aikin kare rayukan al’ummun ta da ma na sauran al’ummun duniya
- Neman Ci Gaban Bai Daya Abu Ne Da Ya Dace Sin Da Amurka Su Maida Hankali A Kai
- Zhao Lijian: Amurka ce kan gaba wajen yiwa kasashen duniya matsin lambar tattalin arziki