Wa Zai Dauki Nauyin Jefa Amurkawa Cikin Wahala A Bikin Kirsimeti?
2021-12-24 21:48:22 CRI
Jaridar The Washington Post ta kasar Amurka ta ruwaito cewa, kungiyar kula da bishiyoyin Kirsimeti ta Amurka ta kiyasta cewa, farashin bishiyoyin Kirsimeti ya karu da kaso 10 zuwa 30 cikin dari a bana, har ma an ba da shawarar cewa, ya fi kyau a sayi bishiyoyin tun da wuri. Kuma manya da kanana dukkansu za su dace da bikin Kirsimeti a bana.
Hauhawar farashin bishiyoyin Kirsimeti, wata alama ce ta karuwar farashin kayayyakin masarufin yau da kullum na Amurkawa. A watan Nuwamban bana, karuwar hauhawar farashin kaya a Amurka ya daga da kaso 6.8 cikin dari, adadin da ya kai matsayin koli a shekaru 39 da suka wuce a Amurka. Kamfanin Bloomberg News ya ruwaito cewa, a farkon watan Disamban bana, Amurkawa fiye da miliyan 21 sun yi fama da karancin abinci.
Duk da haka, farashin hannayen jari, da farashin gidaje dukkansu suna karuwa. Masu kudi suna kara samun kudade. Mujallar Forbes ta zabi biloniyoyi 10 a duniya, wadanda yawan kudadensu ya fi karuwa a shekarar 2021, kuma 6 daga cikinsu ne Amurkawa. Ya zuwa ranar 10 ga wata, jimillar dukiyoyinsu sun karu da dalar Amurka biliyan 304 a shekarar 2021, kana matsakaicin yawan karuwar dukiyoyinsu ya karu da kaso 51 cikin dari.
Annobar COVID-19 tana yaduwa yayin da gibin da ke tsakanin matalauta da masu kudi yake karuwa a Amurka.
Ga alama shan wahalar bikin Kirsimeti, yana da nasaba da hauhawar farashin kaya da yaduwar annobar COVID-19, amma hakika dai dalilan da suka sa haka su ne, ‘yan siyasan Amurka sun gaza wajen yaki da annobar, sun kuma kasa sauke nauyin dake bisa wuyansu, a fannin manufar hada-hadar kudi, kana sun mayar da moriyar siyasa a gaban muradun fararen hula. (Tasallah Yuan)
Labarai Masu Nasaba
- Majalissar Wakilan Jama’ar Kasar Sin Ta Yi Allah Wadai Da Dokar Da Amurka Ta Kafa Mai Lakabin “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”
- Sin Ta Yi Allah Wadai Da Dokar Da Amurka Ta Kafa Mai Lakabin “Haramta Tilastawa Al’ummar Uygur Kwadago”
- Amurka Wadda Ta Kashe Wadanda Ba Su Ji Ba Ba Su Gani Ba Ba Ta Da Matsayin Zargin Wasu Kan Hakkin Dan Adam
- Zhao Lijian: Gwamnatin Amurka ta yi watsi da aikin kare rayukan al’ummun ta da ma na sauran al’ummun duniya