logo

HAUSA

Sin Na Maraba Da ‘Yan Wasa Daga Dukkanin Sassan Duniya Zuwa Gasar Olympics Ta Lokacin Hunturu Ta Beijing

2021-12-20 19:40:56 CRI

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce Sin na maraba da zuwan ‘yan wasan motsa jiki daga dukkanin sassan duniya ciki har da Amurka, halartar gasar Olympics ta lokacin hunturu, wadda birnin Beijing ke daf da karbar bakunci a farkon shekara mai kamawa.

Zhao Lijian, ya ce Sin za ta tabbatar da tsaro, da walwalar ‘yan wasan da za su halarci gasar, kana za ta taimaka musu wajen cimma nasarar da suke fata.

Zhao Lijian ya kara da cewa, al’ummu da kasashe masu yawa a sassan duniya, wadanda suka rungumi ruhin wasannin Olympic, na da buri iri daya, wanda shi ne gudanar gasar ta birnin Beijing cikin nasara. Ko da yake akwai wasu kasashe kalilan dake yunkurin amfani da gasar ta Olympics domin cimma burin siyasa, da karkatar da hankalin duniya daga gaskiya, kuma tabbas irin wadannan kasashe ba za su yi nasara ba.

A cewar babbar jami’ar kwamitin wasannin Olympic na Amurka Sarah Hirshland, Amurkar ta shirya turo ‘yan wasan motsa jikin ta su 230, da kuma masu halartar gasar ajin masu bukata ta musamman 65 zuwa gasar dake tafe.

A wani ci gaban kuma, wasu jami’ai na kwamitocin wasannin Olympic daga kasashen Koriya ta Kudu, da Faransa, da Finland, da Bulgaria, da Girka, da Italiya, da Netherlands, da Sifaniya, da Belarus, da Argentina, da Venezuela, da Cuba, da sauran wasu kasashe da dama, sun bayyana fatan su, na ganin gasar ta birnin Beijing ta gudana lami lafiya. (Saminu)

Saminu