logo

HAUSA

An gudanar da zaben hukumar kafa dokoki ta yankin Hong Kong karo na farko bayan da aka kyautata tsarin zabe a yankin

2021-12-19 17:38:24 CRI

An gudanar da zaben hukumar kafa dokoki ta yankin Hong Kong karo na farko bayan da aka kyautata tsarin zabe a yankin_fororder_1219-1

An fara jefa kuri’un zaben hukumar kafa dokoki ta yankin Hong Kong karo na 7 yau da karfe 8 da rabi da safe, wannan ne karo na farko da aka yi zaben bayan da aka kyautata tsarin zabe a yankin.

Bisa shirin da gwamnatin yankin suka gabatar, za a kammala jefa kuri’un da karfe 10 da rabi na daren ranar, an bude tasoshin jefa kuri’u 630 da tasoshin musamman 24 a dukkan yankin, wadanda suka samarwa masu jefa kuri’u damar yin rajista don jefa kuri’unsu. Kana an kafa tasoshin jefa kuri’u 3 a wurin shiga yankin daga babban yankin kasar Sin don samar wa masu jefa kuri’u na yankin da suke zauna a babban yankin kasar Sin damar jefa kuri’un.

Za a zabi membobi 90 a hukumar kafa dokokin ta yankin a wannan karo. (Zainab)