Kaso kusan 56 bisa dari na Amurkawa na ganin baiken alkiblar kasar
2021-12-17 15:33:04 CMG
Wani sakamakon binciken jin ra’ayin jama’a da jaridar “The New York Post” ta wallafa, ya nuna kaso kusan 56 bisa dari na Amurkawa, basu gamsu da alkiblar da kasar ta sanya gaba ba, musamman bisa la’akari da yanayin tattalin arzikin kasar, da yadda take yaki da cutar COVID-19, da kuma fannin yaki da laifuka.
Binciken ya kuma nuna cewa, kaso 48 bisa dari na Amurkawa da aka yi ra’ayin su, sun bayyana cewa, hankalin su ba ya kwanciya a duk lokacin da suke sayayya, sakamakon yadda wasu bata gari kan lakadawa mutane duka, da harin ‘yan fashi da sauran barayi. Kaza lika kaso 86 bisa dari na Amurkawan na ganin cewa, aikata laifuka sun riga sun zama matsalolin gama gari a Amurka. (Saminu)