logo

HAUSA

Ra’ayoyin Xi Jinping Kan Raya Al'umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan Mutanen Sin Da Afirka

2021-11-28 21:49:30 CRI

Ra’ayoyin Xi Jinping Kan Raya Al'umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan Mutanen Sin Da Afirka_fororder_xjp

Ranar 29 ga wata, Shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai halarci bikin bude taron ministocin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka FOCAC karo na 8 ta kafar bidiyo, tare da gabatar da jawabi. A shekarun baya-bayan nan, a cikin jawabai da dama da Shugaba Xi ya yi kan bunkasa hulda a tsakanin Sin da Afirka, kullum ya kan ambato batun raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan mutanen Sin da Afirka.

A watan Yunin shekarar 2020, yayin da ake fama da annobar cutar COVID-19 a duniya, Xi Jinping ya shugabanci taron kolin musamman tsakanin Sin da Afirka kan yaki da annobar, inda ya ba da shawarwari 4 kan batun hadin gwiwar Sin da Afirka wajen yaki da annobar da jure wahalhalu tare, ya kuma yi alkawarin cewa, kasashen Afirka za su samu alluran rigakafin cutar da zarar kasar Sin ta yi nazari da fara amfani da allurar.

A watan Maris na shekarar 2013, Xi Jinping ya zabi nahiyar Afirka a matsayin wuri na farko da ya ziyarta bayan da ya zama shugaban kasar Sin. A cibiyar taron kasa da kasa na Nyerere da ke kasar Tanzaniya, Xi Jinping ya waiwayi dankon zumunci a tsakanin Sin da Afirka cikin shekaru fiye da 50 da suka wuce, tare da jaddada cewa, har kullum Sin da Afirka na da makomar bai daya. A cikin jawabinsa kuma, karo na farko da ya gabatar da tunaninsa da ra’ayinsa kan manufar Sin kan Afirka, wato “kulla dangantaka da kasashen Afrika bisa gaskiya da kauna da yarda da aminci” da kuma dabarar “cimma muradu da kuma martaba ka'idoji”, wanda ya tsara manufar raya hulda a tsakanin Sin da Afirka a sabon zamani.

Alkaluma sun nuna cewa, kasar Sin ta kwashe shekaru 12 a jere tana matsayin abokiyar ciniki mafi girma a duniya ga Afirka. Tun bayan kafuwar FOCAC, kamfanonin kasar Sin sun shimfida da kyautata hanyoyin layin dogo masu tsawon kilomita dubu 10 ko fiye da haka da kuma hanyoyin mota kusan kilomita dubu 100 a Afirka, sun kuma samar da guraben aikin yi fiye da 4,500,000. Sa’an nan kuma, kasashe 52 na Afirka da kwamitin AU sun daddale takardar yin hadin gwiwar gudanar da shawarar “ziri daya da hanya daya” tare da kasar Sin. Tun bayan barkewar annobar COVID-19, kasar Sin ta samar wa kasashe 53 na Afirka da AU taimakon kayayyaki sau 120 da alluran rigakafin cutar kusan miliyan 200 cikin gaggawa domin yaki da annobar. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan