Moriyar jama’a tana da matukar muhimmanci
2021-11-19 16:52:14 CMG
Dora muhimmanci kan kare moriyar jama’a na cikin muhimman manufofin kasar Sin, wanda ya sa kasar ke kokarin raya tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’a a cikin gida, gami da dukufa wajen haifar da dimbin alfanu ga jama’ar kasashen Afirka, yayin da take hulda da su.
To amma ko wadanne alfanu ne aka samu? Bari in ba ku misali da wasu labaru da na ji a kwanan nan.
A kasar Zimbabwe, hukumar “China Aid” ta kasar Sin, ta haka wasu rijiyoyi 1000 a yankin karkarar kasar, cikin shekarun nan. Kafin haka, mazauna kauyukan kasar su kan debo ruwan sha ne daga cikin kananan tabkuna inda dabbobi suke shan ruwa. Amma yanzu sun samu ruwan sha mai tsabta.
A kasar Sudan ta Kudu, akwai Lily Supermarket, wanda wani basine ya kafa, wurin da a baya karamin kanti ne, amma yanzu ya zama wata babbar kasuwa. A wannan Supermarket ana samar da dimbin ingantattun kayayyaki masu rahusa, gami da guraben aikin yi ga jama’ar kasar. Yanzu kaso 1/3 na darektocin Supermarket din ‘yan kasar Sudan ta Kudu ne.
A kasar Zambia kuwa, koma bayan tattalin arziki sakamakon annobar COVID-19, ya sa kamfanoni da yawa sun kori ma’aikata. A daidai wannan lokaci, taron daukar ma’aikata da kwalejin Confucius mai koyar da Sinanci na jami’ar Zambia (UNZA) ya kira, ya taimaki matasan kasar samun sabbin guraben aikin yi. Yanayin annoba bai hana kasar Sin zuba karin jari ga kasashen Afirka ba, don haka wasu manyan kamfanonin kasar Sin, irin Sinohydro, sun halarci taron don daukar ma’aikata.
Ban da wannan kuma, a kasar Afirka ta Kudu, kamfanin Tencet mai kula da ayyukan yanar gizo ta Internet na kasar Sin, ya zuba kudin da ya kai dalar Amurka miliyan 48 ga kamfanin Ozow na kasar Afirka ta Kudu, ta yadda kamfanin zai iya samar da hidimomi masu alaka da biyan kudi ta wayar salula ga karin miliyoyin mutane.
Wadannan misalai sun nuna cewa, hukumomin kasar Sin, da kamfanonin kasar, da ma mutanen kasar, dukkansu suna kokarin haifar da alfanu ga mutanen kasashen Afirka, yayin da suke zuba jari a wadannan kasashe. Amma ko me ya sa suke yin hakan? Dalili shi ne ra’ayin “amfanar da jama’a” ya riga ya shiga cikin zukatan Sinawa, bayan da kasarsu ta yi shekaru da yawa tana kokarin raya tsarin gurguzu, karkashin jagorancin jam’iyyar Kwaminis ta kasar.
Sa’an nan idan mun yi nazari kan wasu manofofin kasar Sin, da take amfani da su wajen hulda da kasashen Afirka, irinsu “nuna gaskiya, da koyar da fasahohi maimakon samar da kaya kawai”, tushensu shi ne babbar manufar kasar Sin ta “dora matukar muhimmanci kan kare moriyar jama’a”. Yayin da take hulda da sauran kasashe, kasar Sin na da imanin cewa, dole ne a samar da takamaiman alfanu ga mutanen sauran kasashen, idan har ana son ganin wannan huldar hadin gwiwa ta dore.
Cikin shekarun da suka wuce, hadin kan Afirka da Sin ya sa kasashen Afirka samun wasu manyan gine-gine, irinsu madatsar ruwa ta Kaleta ta kasar Guinea, da cibiyar wasannin motsa jiki ta Moi ta kasar Kenya, da dai sauransu. Har ma an sanya hotunan wasu daga cikin wadannan manyan gine-gine kan tsabar kudin kasashen, don nuna yadda kasashen suke samun ci gaba. Sai dai abubuwan da aka fi mai da hankali a kai, yayin da ake hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, su ne tsabtar ruwan sha, da samun guraben aikin yi, da samun saukin sayen kayayyaki na jama’ar kasashen Afirka, da sauran abubuwa da za su tabbatar da ingancin zaman rayuwarsu. Bisa ra’ayin kasar Sin na dora muhimmanci kan moriyar jama’a, duk wani abu da ya shafi moriyar jama’a, mai muhimmanci ne, wanda ya kamata a kula da shi yadda ake bukata. (Bello Wang)