logo

HAUSA

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani dangane da hadin gwiwar ta da nahiyar Afirka

2021-11-26 14:37:44 CMG

Kasar Sin ta fitar da takardar bayani dangane da hadin gwiwar ta da nahiyar Afirka_fororder_1

A yau Juma’a ne kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani, dangane da hadin gwiwar dake tsakanin ta da kasashen nahiyar Afirka a sabon zamani, takardar da ta bayyana muhimmancin huldar hadin kai dake tsakanin bangarorin 2.

Takardar mai taken "Sin da Afirka a sabon zamani: Hadin gwiwar bisa daidaito" ta yi fashin baki kan irin kwarewa da aka samu a baya, da burikan bai daya, da manufofin da suka janyo Sin da kasashen Afirka kusa da juna. Takardar ta kara da cewa, Sin da kasashen Afirka za su ci gaba da zama masu neman cimma makomar bai daya.

Kaza lika takardar ta ce, Sin na daukar burin samar da ci gaba bisa hadin gwiwa da kasashen Afirka, a matsayin jigon manufofin ta na waje, za ta kuma ci gaba da wanzar da wadannan manufofi masu dogon tarihi.  (Saminu)

Saminu