logo

HAUSA

Sabbin Damammaki Da Dabaruntan Sin Sun Kara Azama Kan Farfadowar Cinikayyar Duniya

2021-09-03 21:31:21 CRI

A daren ranar 2 ga wata ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi jawabi ta kafar bidiyo a yayin bikin baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa na kasar Sin na shekarar 2021 (CIFTIS), inda ya sanar da wasu sabbin matakan da kasar ta bulla da su kan kara azama kan ci gaban cinikayyar hidimomi, lamarin da ya dake kara nuna alamar kasar ta ci gaba da bude kofarta ga kasashen duniya. Wannan zai samar da sabbin damammaki wajen farfadowar cinikin hidimomin kasa da kasa, kana kuma zai fito da kyawawan dabaru wajen daidaita matsalolin tattalin arzikin duniya.

Matakan da kasar Sin ta sanar a bana, sun shafi kara bude kofarta ga ketare, habaka fannonin yin hadin gwiwa, kyautata kafa ka’idojin ba da hidima, da ci gaba da goyon bayan bunkasar kanana da matsakaitan masana’antu. Yayin da annobar COVID-19 take ci gaba da addabar al’ummar duniya, kuma tattalin arzikin duniya bai farfado kamar yadda ake zato ba, yadda kasar Sin ta rika kara azama kan bude kofarta ta fuskar aikin ba da hidima ga ketare, ya kasance kuzari mai muhimmanci wajen farfado da cinikayyyar kasa da kasa da kuma bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Abun lura shi ne, yawan masana’atun da suka halarci bikin na bana a zahiri ya karu da kaso 6 cikin dari bisa na bikin da ya gabata, yayin da yawan kamfanoni masu karfi a duniya ya karu da kaso 9 cikin dari. Wannan ya nuna cewa, kariyar cinikayya da ra’ayin kashi kai ba su samu amincewar jama’a ba. Kuma hakan ba zai iya warware matsalolin da ake fuskanta a fannonin tattalin arzikin duniya, cinikin kasa da kasa da zuba jari ba, kamata ya yi a samu ci gaba cikin lumana ta hanyar yin hadin gwiwa domin samun nasara tare. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan