logo

HAUSA

Ingantuwar hadin gwiwa kan shawarar “Ziri daya da hanya daya” ta karfafa farfadowar tattalin arzikin duniya

2021-08-09 14:52:06 cri

Sabbin alkaluman da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar sun nuna cewa, daga watan Janairu zuwa Yuli na wannan shekarar, jimillar kudin da aka samu daga kayayyakin da aka shigo da su da wadanda aka fitar a tsakanin kasar Sin da kasashen dake bin shawarar “Ziri daya da hanya daya”, sun kai Yuan tiriliyan 6.3, adadin da ya karu da kashi 25.5%. Kuma daga cikin su, adadin da kasar ta fitar na kaya ya karu, da kashi 25.3% yayin da aka shigo da kaya da darajar adadin sa ta karu da kashi 25.7%.

Kwanan baya, a yayin taron da ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya gudanar, an gabatar da yin tsayin daka kan bude kofa ga kasashen ketare, tare da yin kwaskwarima a cikin gida, da inganta raya shawarar “Ziri daya da hanya daya” yadda ya kamata cikin hadin kai.

Masu aiki da nazari a fannin sun yi imanin cewa, hadin gwiwar da ake yi bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ya karfafa mu’amala da musaya a tsakanin kasa da kasa, sannan kuma ya sanya karfi kan farfado da tattalin arzikin duniya, a yayin da ake tinkarar annobar numfashi ta COVID-19.

A matsayinsa na babban aikin hadin gwiwa game da shawarar "Ziri daya da hanya daya", layin dogo na Lagos-Ibadan, wanda ya kasance layin dogo na zamani na farko dake yammacin Afirka da kamfanin kasar Sin ya gina, ya soma aiki a kwanan nan. Wannan layin dogo ya hada Lagos, birni mafi girma a Afirka, kuma cibiyar tattalin arzikin Najeriya, da Ibadan, babban birnin masana'antu a kudancin kasar, ya kuma kyautata yanayin sufuri a kudancin Najeriya, kana da bude babbar hanyar ci gaban tattalin arzikin cikin gidan kasar. Malam Sac, wani mazaunin yankin ya yi matukar farin ciki lokacin da ya hau jirgin kasar, ya ce,

“Hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Najerriya da Sin na da kyau sosai. Kasar Sin ta yi iyakacin kokarin ta. Ina fatan za ta kara kawo wa Najeriya fasahohin da suka shafi ayyukan ginawa, da gudanarwa a fannonin layin dogo.”

A cikin ‘yan watannin nan, an samu sauyin yaduwar nau’in COVID-19 na Delta, kuma annobar numfashi ta COVID-19 na ci gaba da yaduwa. Amma duk da haka a wannan yanayin da muke ciki, jiragen kasa a tsakanin Sin da Turai yana ta habaka, kuma adadin tafiyar da jiragen ya kai wani sabon matsayi a cikin wata guda. A cikin watanni shida na farkon wannan shekarar, yawan tafiyar da jiragen kasan ya zarce sau 7,300, wato ya karu da 43% bisa na makamancin lokacin bara, kana jimillar kayayyakin da suka yi jigila ta kai mizanin TEU dubu 701, ciki kuwa har da da kayayyakin rigakafi da shawo kan cutar tan dubu 96.

Ban da wannan kuma, bude aikin sabon jirgin kasa, ta warware wasu matsaloli cikin gaggawa. Jirgin kasa na farko na kasa da kasa a tsakanin Qingdao-Dushanbe ya riga ya fara aiki a wannan shekarar.

Jakadan Jamhuriyar Tajikistan a kasar Sin Saidzoda Zohir, yana ganin cewa, wannan jirgin kasa zai yi tasiri mai kyau wajen inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, a fannonin tattalin arziki da cinikayya. Ya ce,

“Ina ganin cewa, bude wannan sufurin jirgin kasa yana da matukar mahimmanci, musamman kasancewar hakan zai iya haifar da karin hadin gwiwa a tsakanin kasashen dake bin shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ta jiragen kasa masu daukar kaya a cikin tsarin “Ziri daya da hanya daya”. Wannan jirgin kasa ya nuna karuwar hadin gwiwa a tsakanin Tajikistan da Sin a fannin tattalin arziki da cinikayya, kuma na yi imanin cewa, zai taimakawa Tajikistan wajen farfado da ci gaban tattalin arzikin kasa cikin sauri.”

A cikin shekaru 8 da suka gabata, da fara gabatar da shawarar "Ziri da Hanya daya", shawarar ta kawo babbar dama da riba ga kasashe daban daban. Yawan kasashen da suka kulla yarjejeniyar hadin gwiwa bisa shawarar tare da kasar Sin sun kai 140. Har ila yau, jimillar cinikayya da aka yi tsakanin Sin da abokan cinikayyarta bisa shawarar ya wuce dalar Amurka tiriliyan 9.2, kuma jimillar jarin da kamfanonin Sin suka zuba kai tsaye a kasashen da abin ya shafa ya wuce dalar Amurka biliyan 130. Ko shakka babu shawarar “Ziri daya da hanya daya”, ta zama wani babban dandalin hadin gwiwa na kasa da kasa mafi girma a duniya.

Madam Prazeres, tsohuwar ministar kula da tattalin arziki da cinikayya da ketare ta kasar Brazil, a kwanan nan ta bayyana cewa, shawarar hadin gwiwa ta “Ziri daya da hanya daya” tana da mahimmanci sosai ga farfado da tattalin arzikin duniya a halin da ake ciki yanzu. Ta ce,

“Shawarar ‘Ziri daya da hanya daya’ tana iya farfado da tattalin arziki. Zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa, da kiyaye cudanya, suna da tasiri mai muhimmanci ga wata kasa. Za su iya ba da taimako ga sassa daban daban, da ayyukan tattalin arziki daban daban, ta yadda za a iya taimakawa wannan kasa ta murmure daga cutar.” (Mai fassara: Bilkisu Xin)