logo

HAUSA

Najeriya ta yi hasarar jarin da ya kai dala biliyan 50 saboda cushewar bangaren mai

2021-08-19 10:46:27 CRI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kasar ta yi hasarar kudaden jarin da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 50 a cikin shekaru 10, saboda rashin tabbas, da rashin sanya hannu kan dokar inganta bangaren man fetur (PIB), da kuma rashin ci gaba, da ma cushewar bangaren man fetur din.

A farkon wannan makon ne dai, shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar, wadda aka tsara da nufin yi wa bangaren man gyaran fuska, da janyo masu sha’awar zuba jari a bangaren mai da iskar gas, tare da barin kasuwa ta yi halinta a bangaren farashin albarkatun man fetur.

Matakin fadar shugaban kasar kan wannan doka, ya kasance tarihi, ganin yadda ake jiran fara aiki da wannan doka tun kimanin shekaru 20. Dokar ta fayyace matakai na shari’a, da tsarin gudanarwa, da ma yadda za a tafiyar da bangaren man kasar, da raya al’ummomin da ake hakar man a yankunansu, da sauran batutuwan da abin ya shafa.

Shugaban ya kuma bayyana yayin bikin sanya hannu kan sabuwar dokar da ya gudana jiya Laraba cewa, cushewar bangaren man, ya shafi ci gaban tattalin arziki, inda ya buga misali da rashin kudiri na siyasa a bangaren gwamnatocin da suka gabata, wajen tabbatar da samun sauyi.(Ibrahim)

Ibrahim