logo

HAUSA

Bankin duniya ya sanya Najeriya cikin jerin kasashen da suke da hadarin bashi

2021-08-12 11:33:12 CMG

Bankin duniya ya sanya Najeriya cikin jerin kasashen da suke da hadarin bashi_fororder_3

Jaridar Punch da ake wallafawa a Najeriya ta watsa wani labari dake cewa, hadaddiyar kungiyar samar da ci gaba ta kasa da kasa, a karkashin bankin duniya, ta gabatar da rahoton hada hadar kudi na shekarar 2021 a ranar Litinin, inda ta sanya Najeriya cikin kasashe 10, mafi fama da hadarin bashi.

An ce yawan bashin da ake bin Najeriya ya kai dalar Amurka biliyan 11.7, inda ta kasance ta biyar a duniya a fannin fama da matsalar bashi. Sauran kasashe 4 da ke gaban Najeriya wajen fama da matsalar su ne Indiya, da Pakistan, da Bangladesh, da kuma Vietnam.

Zuwa ranar 30 ga watan Yunin bana, yawan bashin da bankin duniya ya ba Najeriya, wanda ba ta fara yin amfani da shi ba tukuna, ya kai kimanin dala biliyan 8 da miliyan 656. (Bello Wang)

Bello