logo

HAUSA

An kashe mutane 22 a wani hari a yankin Tsakiyar Najeriya

2021-08-15 15:58:58 CMG

An kashe mutane 22 a wani hari a yankin Tsakiyar Najeriya_fororder_0815-filato-Ibrahim

Rahotanni daga Najeriya na cewa, a kalla mutane 22 ne suka gamu da ajalinsu, kana wasu 14 suka jikkata, a wani hari da wasu masu dauke da makamai suka kai ranar Asabar da safe a jihar Filato, dake yankin tsakiyar kasar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Filato Ubah Ogaba, ya bayyana cikin wata sanarwa a wannan rana cewa, wasu masu dauke da matakai ne a kan hanyar Rukuba a karamar hukumar Jos ta arewa, su ka kaiwa wasu jerin gwanon motocin bas 5 dauke da musulmi hari, inda suka kashe mutane 22 kana wasu 14 kuma suka jikkata.

Ogaba ya ce, wadanda lamarin ya rutsa da su dai, suna dawo wa ne daga wani taron Zikri da aka yi a jihar Bauchi, a kan hanyarsu ta komawa Ikare dake jihar Ondo, inda wasu gungun mahara da ake zaton ‘yan kabilar Irigwe ne suka kai musu hari. Ya ce, bayan samun kiran neman taimakon gaggawa, nan da nan an tura tawagar jami’an ‘yan sanda da sojoji da sauran hukumomin tsaro, zuwa wurin da lamarin ya faru, inda kuma aka yi nasarar ceto mutane 21 tare da kama mutane 6 da ake zargi.

Kakakin ya ce, yanzu haka dai, ana gudanar da bincike, don zakulo sauran wadanda ke da hannu a wannan danyen aiki. A don haka, ya bukaci al’ummomin dake yankin, da su kwantar da hankalinsu, su kuma taimakawa ‘yan sanda da muhimman bayanai a binciken da ake yi. (Ibrahim)

Ibrahim