logo

HAUSA

Abubuwa masu guba da suka rage cikin shekaru da dama su kan yi illa ga lafiyar ‘yan tayi

2021-08-17 07:19:42 CRI

Abubuwa masu guba da suka rage cikin shekaru da dama su kan yi illa ga lafiyar ‘yan tayi_fororder_src=http___www.lovehhy.net_lib_img_9378235_1322407_1412064310&refer=http___www.lovehhy

Wani sabon nazari ya shaida mana cewa, abubuwa masu guba da suka rage cikin kasa da ma muhallin halittu cikin goman shekaru idan sun shiga cikin jikin masu juna biyu, to, duk da cewa kadan ne, amma su kan yi illa ga yadda ‘yan tayi suke girma yadda ya kamata. Wadannan abubuwa masu guba sun hada da maganin kashe kwari na DDT, sinadaran PCB, takin zamani mai kunshe da sinadarin organochlorine da dai sauransu.

Masu nazari daga kwalejin nazarin lafiyar kananan yara da yadda ‘yan Adam suke girma na kasar Amurka, sun kaddamar da wani bayani a kwanan baya cewa, sun tantance samfuran jini da aka tattara daga Amurkawa masu juna biyu dubu 2 da dari 2 da 84, tare da yi musu binciken B ultrasound, wato daukar hoton sassan jiki, don sa ido kan yadda ‘yan tayinsu suke girma a cikinsu. Wadannan masu juna biyu sun shiga nazarin ne yayin da suka cika watanni 3 da samun ciki. Masu nazarin sun gano cewa, yawan abubuwa masu guba da ke cikin jinin wadannan masu juna biyu, ya yi illa ga yadda ‘yan tayinsu ke girma.

Alal misali, idan akwai sinadarin PCB da yawa a cikin jikin masu juna biyu, to, matsakaicin girman kawunan ‘yan tayi da ke cikin cikinsu ya yi kasa da milimita 6.5, gwargwadon girman kawunan ‘yan tayi da ke cikin masu juna biyu wadanda ba su da sinadarin PCB da yawa a jiki. Haka kumu, idan akwai takin zamani mai kunshe da sinadarin organochlorine da yawa a cikin jikin masu juna biyu, to, matsakaicin girman kawunan ‘yan tayi da ke cikinsu, ya yi kasa da milimita 4.7, gwargwadon girman kawunan ‘yan tayi da ke cikin masu juna biyu wadanda babu takin zamani mai kunshe da sinadarin organochlorine da yawa a jikinsu. Duk da haka ya zuwa yanzu, masu nazarin ba su san ko yadda ‘yan tayin ba su girma yadda ya kamata, zai yi illa ga yadda suke girma bayan da aka haife su ko a’a ba.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, ko da yake an riga an haramta yin amfani da yawancin abubuwa masu dauke guba da suka yi amfani da su cikin nazarinsu yanzu, wadanda aka fara hana yin amfani da wasu daga cikinsu kusan goman shekaru da suka wuce, amma da wuya abubuwa masu guba da suka rage cikin muhallin halittu su iya bacewa, mutane su kan taba wadannan abubuwa masu guba ta hanyoyin cin abinci, da sha ta cikin ruwa, kuma ya zuwa yanzu sun yi illa ga lafiyar bil’Adama.   (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan