logo

HAUSA

An Yiwa Mutane Alluran Riga kafin COVID-19 Sama Da Biliyan 1.8 A Kasar Sin

2021-08-11 18:52:56 CRI

Hukumar lafiya ta kasar Sin ta sanar Larabar nan cewa, ya zuwa jiya Talata, an yi wa mutane alluran riga kafin annobar COVID-19 sama da biliyan 1.8 a fadin kasar. Kasar Sin dai ta kara daukar matakan hana yaduwar cutar a asibiti, da karfafa yin gwaji, yayin da kasar ke sake samun bullar masu kamuwa da cutar a cikin gida.

Shugaban hukumar lafiya ta kasar Ma Xiaowei, ya bayyana cewa, ya kamata a koda yaushe a ba da muhimmanci ga aikin dakile yaduwar cutar, yana mai gargadi da a kara daura damara wajen yaki da cutar. (Ibrahim)

Ibrahim