Kamfanin Huawei ya lashi takobin taimakawa nahiyar Afrika
2021-07-27 10:38:22 CRI
Kamfanin sadarwa na Huawei na kasar Sin zai kasance a kan gaba wajen karfafa kokarin sauya nau’o’in makamashi masu gurbata muhalli a nahiyar Afrika ta hanyar fasahohin zamani.
Daraktan kula da sashen fasahohin samar da makamashi a kudancin Afrika na kamfanin Huawei, Huang Su, ya ce cin gajiyar sabbin fasahohi shi ne jigon bunkasa samar da makamashi mai tsafta da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba.
Ya ce fasahohin zamani za su iya ba da gaggarumin taimako wajen tabbatar da samar da wadataccen lantarki ga kowanne gida da harkar kasuwanci a Afrika.
Kididdiga daga hukumar kula da makamashi ta duniya IEA, ta nuna cewa, mutane miliyan 580 a yankin kudu da hamadar Sahara ne ke fama da rashin lantarki a shekarar 2019.
Huang ya kara da cewa, amfani da dimbin makamashin da ake iya sake amfani da shi da ake sa ran zai bayar da gudunmuwar kaso 22 na jimilar makamashin da za a yi amfani da shi zuwa shekarar 2022, zai gaggauta tabbatar da cimma ajandar nahiyar. (Fa’iza Mustapha)
Labarai Masu Nasaba
- Firaministan kasar Sin ya jaddada bukatar aiwatar da dukkanin matakai na shawo kan ambaliyar ruwa da ba da agajin jin kai
- Sojojin Kamaru sun hallaka mayakan Boko Haram 20
- Mazauna Zhejiang suna kokarin ceton kansu yayin da suke fama da mahaukaciyar guguwa
- Sin ta bukaci a dauki matakin gaggawa na koli kan yanayi mai tsanani