logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya jaddada bukatar aiwatar da dukkanin matakai na shawo kan ambaliyar ruwa da ba da agajin jin kai

2021-07-27 10:37:10 CRI

Firaministan kasar Sin ya jaddada bukatar aiwatar da dukkanin matakai na shawo kan ambaliyar ruwa da ba da agajin jin kai_fororder_210727-saminu 2-Li Keqiang

A jiya Litinin, firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada kira ga daukacin sassan masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen aiwatar da dukkanin matakai na shawo kan ambaliyar ruwa, da ba da agajin jin kai ga wadanda ibtila’in ambaliyar ta shafa, tare da mayar da kare rayukan al’umma da dukiyoyin su gaban komai.

Li ya yi wannan tsokaci ne yayin da yake jagorantar taron jami’ai ta kafar bidiyo, daga helkwatar hukumar shawo kan ambaliyar ruwa da fari dake nan birnin Beijing.

Firaministan ya ce ruwan sama mai karfi da ke sauka a baya bayan nan, ya haifar da babbar asara ga wasu sassa na kasar Sin, don haka ya zama wajibi a dauki cikakkun matakan kandagarki, na rage asarar da mamakon ruwan sama ke haddasawa musamman a arewacin kasar, da ma mahaukaciyar iska mai hade da ruwan sama dake fadawa yankunan bakin tekun kasar.

Ya ce da farko, ya zama wajibi a dage da aikin ceton al’ummun da suka rasa matsuguni, kana a samar da agajin jin kai a yankunan da ibtila’in ya fi shafa, ciki har da lardin Henan. Kana a gaggauta tura tawagogin kwararru da kayayyakin aiki, tare da fitar da bayanai a bude, ba tare da boye komai ba.

Kaza lika Li ya ce akwai bukatar karfafa ayyukan da ke da rauni a fannin shawo kan bala’in, ta yadda za a kai ga cimma nasarar ayyukan gaggawa, da na fadakar da al’umma game da matakan kare rayukan su.

Bugu da kari, ya yi kira da a kara azama wajen ceton rayukan al’ummar da bala’in ya fadawa, da karfafa fannin kiwon lafiya, da dakile barkewar cututtuka, da gaggauta yashe magudanan ruwa, da dawo da makamashi, da ruwan sha, da hanyoyin sufuri, da na sadarwa cikin hanzari.

Daga nan sai ya bayyana aniyar gwamnati, ta fitar da biliyoyin kudi daga asusun tsumi na kasa, domin tallafawa yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa, ta yadda za su cimma nasarar gudanar da muhimman ayyukan farfadowa, da wadanda za a bukata, don sake gina yankuna bayan wucewar bala’in. (Saminu)